COVID: Za a sallami wasu da su ka samu sauki a asibiti – Inji Ministan lafiya

COVID: Za a sallami wasu da su ka samu sauki a asibiti – Inji Ministan lafiya

Mun samu labari cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwar cewa za a kara sallamar wasu da ke jinyar cutar Coronavirus, su bar asibiti su koma gidajensu.

Ministan lafiya na Najeriya, Dr. Osagie Ehanire ya bayyana cewa da zarar sakamakon gwajin da aka yi wa marasa lafiyar ya nuna sun warke, za a sallamesu daga asibiti.

Dr. Osagie Ehanire ya ce za a sallami wadanda ke kwance a gadajen asibiti ne idan har gwaji ya nuna cewa ba su dauke da kwayar cutar COVID-19 a jikinsu a halin yanzu.

An rahoto Ministan ya na cewa: “An sallami mutane biyar, sun tafi gida. Abin takaicin shi ne Najeriya ta samu mutuwar marasa lafiya biyu (masu cutar COVID-19).”

Ministan kasar ya kara da cewa: “Dukkaninsu su na dauke da wasu cututtukan a jikinsu.” Daga nan sai ya ke albishir: “Akwai wasu Marasa lafiyan da za a sallama.”

KU KARANTA: Buhari zai tallafawa Marasa karfi miliyan 11 a lokacin annoba

COVID: Za a sallami wasu da su ka samu sauki a asibiti – Inji Ministan lafiya
Ministan lafiya Osagie Ehanire ya ce wasu masu jinya za su koma gida
Asali: UGC

“Wasu ‘yan tsirarrru daga cikin masu jinyar sun cancanci a sallamesu, su tafi gida, sai dai dokar ita ce dole sai an yi masu gwaji sau biyu, an ga ba su dauke da cutar.”

Osagie Ehanire ya nuna cewa za ayi wannan gwaji ne har sau biyu a cikin sa’a 24 zuwa 48. Watau za a yi wa masu gwajin COVID-19 biyu a cikin kwana guda ko biyu.

“Idan har gwajin bai nuna cutar ba ta jikinsu ba, sai a cigaba da rike su. Jinyar ta kan dauki wata guda ko kuma makonni uku zuwa biyar, ya danganta da jikin mutum.”

Da ya ke yi wa ‘Yan jarida jawabi a Ranar Talata, 31 ga Watan Maris, Osagie Ehanire ya nuna cewa wasu su kan samu sauki da wuri, alhali wasu sai sun yi doguwar jinya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng