An kama wani da bindigu da alburusai cikin buhun garin rogo (Hoto)

An kama wani da bindigu da alburusai cikin buhun garin rogo (Hoto)

Rundunar 'yan sanda na jihar Niger ta kama wani mutum da aka kama dauke da bindigu ba bisa ka'ida ba a Minna.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Adamu, wanda ya fitar da sanarwar a Minna ranar Talata ya ce bayan an tsegunta wa 'yan sandan, tawagar jami'an SARS da ke yankin sun kama wani Danjuma Toko dan shekara 25 a garin Zuru na jihar Kebbi.

Kwamishinan ya ce, "A ranar 22 ga watan Maris misalin karfe 8 na dare bayan samun bayanai, jami'an tawagar SARS sun kama wani Danjuma Toko, na miji dan shekara 25 a garin Zuru na jihar Kebbi a tashan mota na Kontagora da ke shataletalen Mobil a Minna, da suke bincika jakunkunansa sun gano bindigu shida da alburusai 18 da ake boye cikin buhun gari rogo."

An kama wani da bindigu da alburusai cikin buhun garrin rogo (Hoto)

An kama wani da bindigu da alburusai cikin buhun garrin rogo (Hoto)
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Shugaban 'Yan sandan Najeriya

Adamu ya ce wanda ake zargin ya bayyana cewa wani Paul ne a Ogoja a jihar Cross Rivers ya bashi domin ya kaiwa 'yan uwansa Kabiru Kanda da Dauda Kanda da ke zaune a garin Zuru na Kebbi.

Ya kara da cewa, "a lokacin da ake masa tambayoyi, ya bayyana cewa wani Paul ne a Ogoja a jihar Cross Rivers ya bashi domin ya kaiwa yan uwansa Kabiru Kanda da Dauda Kanda (dukkansu maza) da ke zaune a jihar Kebbi. Za a gurfanar da shi a kotu nan ba da dade wa ba."

Kwamishinan ya yi kira ga al'ummar jihar su rika taimakawa jami'an tsaro da bayyanai game da miyagu da ke zaune a cikinsu.

A wani rahoton, kun ji cewa mazauna gidan gyaran hali a jihar Kaduna sun yi yunkurin balle gidan gyaran halin bayan rikici ya barke a kan barkewar cutar coronavirus a kasar nan, jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

'Yan gidan gyaran halin, wadanda suka ji tsoron samun cutar sakamakon rashin isasshiyar iska mai tsafta da kuma kayan kariya daga cutar, sun taru da yawansu a safiyar yau Talata inda suka yi yunkurin ballewa su tsere daga gidan gyaran halin.

Jami'an tsaro da suka dinga harbi a farfajiyar gidan gyaran halin don tsorata 'yan gidan gyaran halin tare da saisata komai. A halin yanzu mutum daya ne ake tsammanin ya rasa ransa sakamakon rikicin amma jami'ai masu yawa sun samu raunika inda aka gaggauta mika su asibiti don taimakon likitoci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel