Ban san takamamen inda Abba Kyari ya ke ba a halin yanzu - Abayomi

Ban san takamamen inda Abba Kyari ya ke ba a halin yanzu - Abayomi

Kwamishinan Lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya yi karin bayani a kan lafiyar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Mallam Abba Kyari da aka gano yana dauke da coronavirus a makon da ta gabata.

Abayomi ya bayyana cewa bai san inda Abba Kyari ya ke ba a halin yanzu amma ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar yana lafiya kuma yana cikin farin ciki a lokacin da suka yi hira ta manhajjar Whatsapp kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

Kwamishinan yayin amsa tambayoyin manema labarai a ranar Talata 31 ga watan Maris ya ce;

"Ban tsan tsarin tafiye-tafiyen shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ba saboda haka ban san inda ya ke ba a yanzu.

Ban san inda Abba Kyari ya ke ba amma da alamun yana cikin annashuwa da kuzari - Farfesa Abayomi

Ban san inda Abba Kyari ya ke ba amma da alamun yana cikin annashuwa da kuzari - Farfesa Abayomi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Shugaban 'Yan sandan Najeriya

"Mun gaisa amma ta Whatsapp amma kuma ba za ka iya sanin inda mutum ya ke ba ta whatsapp.

"Muna magana lokaci zuwa lokaci amma ban tambayi inda ya ke ba. Bisa alamu yana cikin koshin lafiya da farin ciki kuma muna tattaunawa ne a kan batuttuwan da suka shafi tsare-tsare saboda haka ya dade da muka yi magana game da lafiyarsa saboda haka ina tsamanin ya warke."

Idan ba a manta ba shugaban fadar shugaban kasar Abba Kyari ya tabbatar da cewa ya kamu da kwayar cutar coronavirus kuma za a tafi da shi Legas a ranar 29 ga watan Maris domin a sake masa wasu gwaje-gwaje da kuma kulawa.

Ya kuma kara da cewa baya fama da zazzabi da kuma sauran alamomin da masu kwayar cutar ke da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel