Yobe: Buni da Gubana za su yi amfani da rabin albashinsu wajen yakar annobar COVID-19

Yobe: Buni da Gubana za su yi amfani da rabin albashinsu wajen yakar annobar COVID-19

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, da Mataimakinsa watau Idi Barde Gubana, sun bada 50% daga cikin albashinsu a matsayin tallafi na yaki da cutar COVID-19.

Kwamishinan harkokin cikin gida da yada labarai da al’adu na jihar Yobe, Abdullahi Bego ya bada wannan sanarwa a wani jawabi a Ranar Talata, 31 ga Watan Maris, 2020.

Abdullahi Bego wanda shi ne kuma Sakataren wani kwamiti na musamman da gwamnatin Yobe ta kafa domin yakar annobar COVID-19 ya shaidawa Daily Trust wannan.

Bayan wannan kokari da Mai girma gwamna da mataimakinsa su ka yi, Sakataren gwamnatin Yobe da shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnatin jihar sun bi sahunsu.

Haka zalika shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Yobe ya bada 50% na albashinsa a matsayin gudumuwar yaki da wannan cuta ta Coronavirus da ke hallaka Bayin Allah.

KU KARANTA: Cutar Coronavirus ta aika mutane 40, 000 barzahu a fadin Duniya

Yobe: Buni da Gubana za su yi amfani da rabin albashinsu wajen yakar annobar COVID-19
Gwamna Buni da Gubana da Manyan Jihar Yobe sun bada tallafin yaki da COVID-19
Asali: Facebook

Bego ya kara da cewa:

“Duka Sakatarorin din-din-din, shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnati, manyan Sakatarori da shugabannin hukumar ma’aikatan kananan hukumomin, hukumar majalisa da Alkalai da ta Malaman kimiyya da fasaha, hukumar zabe ta jiha, hukumar ilmin larabci da musulunci, hukumar bada kwangila, hukumar aikin hajji da walwalar Alhazai, da kuma Darektocin da ke kananan humomi 17 na jihar Yobe za su bada 50% na albashinsu wajen ganin an yaki annobar COVID-19." Yanzu dai annobar ba ta kai ga shigowa jihar ba tukuna.

Sakataren wannan asusu ya bayyana cewa Kakakin majalisar dokokin Yobe, Hon. Ahmed Lawan Mirwa da mataimakinsa, Hon. Mohammed Auwal Isa sun yi na su hobbasan.

Shugabannin majalisar da kuma duk sauran ‘Yan majalisa 22 za su bada rabin albashin na su. Alkalin Alkalan jihar da kuma Grand Khadi sun kyautar da rabin albashinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel