Gwamnatin tarayya ta sake rage farashin litar man fetur a karo na biyu

Gwamnatin tarayya ta sake rage farashin litar man fetur a karo na biyu

Gwamnati tarayya ta sanar da sake farashin litar man fetur zuwa N123.50 kowacce lita daya.

A wani jawabi da hukumar kula da farashin man fetur (PPPRA) ta fitar da yamacin ranar Talata, sakataren hukumar, Mista Abdulkadir Saidu, ya ce rsabon farashin litar man zai fara aiki ne daga ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2020.

A cewar jawabin, "bisa dogaro da sabon tsarin duba farashin man fetur a gidajen mai kowanne wata, mu na sanar da rage farashin litar man fetur zuwa N123.50.

A ranar 19 ga watan Maris ne gwamnatin tarayya ta rage farashin litar man fetur daga N145 zuwa N125 sakamakon karyewar farashin danye man fetur a kasuwar duniya saboda annobar coronavirus.

"Sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilu, 2020, kuma ya shafi dukkan gidajen man fetur da ke fadin Najeriya," a cewar jawabin.

Gwamnatin tarayya ta sake rage farashin litar man fetur a karo na biyu

Gwamnatin tarayya ta sake rage farashin litar man fetur a karo na biyu
Source: UGC

Jawabin ya kara da cewa, PPPRA da sauran hukumomin da suka dace za su dauki matakan tabbatar da cewa an yi wa sabon tsarin biyayya tare da yin kira ga jama da duk kamfanonin dillancin man fetur a kans su bawa gwamnati hadin kai wajen ganin sabon farashin ya fara aiki a kan lokacin da aka bayyana.

DUBA WANNAN: Ba daidai bane a yi amfani da sojoji don tilasta jama'a su zauna a gida - Falana

Ko a ranar Litinin sai da Legit.ng ta wallafa rahoton cewa Sadiya Farouk, ministar walwala da jin dadin 'yan kasa, ta ce ma'aikatarta ta fara tura kudi ga gidaje masu matukar talauci a fadin kasar nan don rage musu radadin takurar bullowar cutar coronavirus.

Ministar ta sanar da hakan ne a yayin jawabi ga manema labarai a Abuja, a ranar Litinin.

Farouk ta ce ma'aikatarta ta fara biyan gidajen da aka sani cewa suna fama da tsananin talauci kuma ake tallafa musu har da basu albashi kowanne wata.

Ta ce sauran rukunin jama'ar da za a tallafawa sun hada da karin matalauta a yayin da ake fama da annobar cutar corona mai sarke numfashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel