COVID-19: Sanatoci da ‘Yan Majalisar Jihar Kano sun yi hobbasa

COVID-19: Sanatoci da ‘Yan Majalisar Jihar Kano sun yi hobbasa

Yayin da ake cigaba da yakar cutar Coronavirus a Najeriya da sauran kasashen Duniya, gwamnatoci da masu hali su na ta faman yin bakin kokarinsu.

A jihar Kano, Mai girma gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kafa gidauniya ta musamman inda Attajiran jihar da masu mulki su ka bada gudumuwarsu.

Daga cikin wadanda su ka zuba kudi a cikin wannan asusu akwai ‘Yan majalisar wakilan tarayya da ‘yan majalisar dattawan da ke wakiltar duk Mazabun Kano.

Barau Jibril wanda ke wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa shi ne wanda ya fi bada kudi mafi tsoka, inda ya zuba Naira miliyan hudu a asusun da aka kafa.

Tsofaffin gwamnonin jihar Kano kuma Sanatoci a yanzu, Malam Ibrahim Shekarau da Arch. Kabiru Ibrahim Gaya, duk sun bada gudumuwar Naira miliyan biyu.

KU KARANTA: Watakila a kara kudin wuta ana cikin fama da annobar Coronavirus

Ibrahim Shekarau shi ne mai wakiltar Mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa. Haka zalika Kabiru Gaya ya na wakiltar Yankin Kudancin jihar Kano a majalisar.

Sauran ‘Yan majalisar wakilan tarayya da ake da su a jihar sun bada gudumuwarsu. Wasu ‘yan majalisar wakilai 11 na jihar Kano sun bada Naira miliyan dai-daya.

Ragowar ‘yan majalisa 13 da ake da su daga sauran Mazabu sun hadu sun bada Naira miliyan uku. ‘Yan majalisar jihar sun ajiye duk wani banbancin siyasarsu a gefe.

Gaba daya dai abin da aka samu daga hannun wadannan ‘Yan majalisa shi ne Naira miliyan 22. Darektan yada labarai na gwamnatin jihar Kano ya bayyana wannan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel