Ba daidai bane a yi amfani da sojoji don tilasta jama'a su zauna a gida

Ba daidai bane a yi amfani da sojoji don tilasta jama'a su zauna a gida

Femi Falana, babban lauya mai rajin kare hakkin bil Adam, ya ce babu dokar da ta amince a yi amfani da sojoji don hana jama'a walwala a kan annoba.

A jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ga 'yan Najeriya a ranar Lahadi, ya bada umarnin rufe jihohin Ogun, Abuja da Legas daga karfe 11 na daren Litinin har zuwa yadda hali yayi.

Amma kuma Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ogun, ya ce yayi nasarar shawo kan shugaba Buhari a kan kara kwanakin zuwa ranar Juma'a ta yadda za a samu wadataccen kayan abinci.

Jama'a da dama sun dinga kalubalantar hukuncin Buhari na hana walwala a jihohin saboda wasu lauyoyin sun ce babu hakan a shari'ance.

Amma kuma shugaba Buhari daga baya ya saka hannu a kan dokar killacewar.

Ba daidai bane a yi amfani da sojoji don tilasta jama'a su zauna a gida
Femi Falana
Asali: UGC

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Maris, 2020.

A takardar da Falana ya fitar, ya ce a yayin da shugaban kasar ke da karfin ikon hana yawo a jihohin don hana yaduwar cutar coronavirus, wannan tsarin za a tabbatar da shi ne ta hanyar amfani da karfin rundunar soji.

DUBA WANNAN: Sarki mai daraja ta daya a Najeriya ya bayyana tsirrai 2 da ke maganin cutar coronavirus

"Bayan jawabin da shugaba Buhari yayi a kan cutar coronavirus, wasu lauyoyi sun dinga tuhumar inda kundin tsarin mulkin kasar nan ya bada damar haramta yawo a Abuja, Legas da Ogun saboda barkewar cuta.

Babu shakka shugaban kasar na da damar daukar matakan da za su hana yaduwar cutar amma kuma matakan dole ne su yi biyayya ga sashi na 305 na kundun tsarin mulki. Sai dai kuma idan 'yan sanda ba za su iya tabbatar da shi ba.

"Amma kuma yayin da ake jinjinawa sojin kasar nan da suka bada kayan kiwon lafiyan su don amfanin farar hula, shirin sa su hana yawo bai kamata ba." Falana ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel