Yaki da ta’addanci: Sojojin Najeriya sun kashe kwamandan Boko Haram, Abu Usamah

Yaki da ta’addanci: Sojojin Najeriya sun kashe kwamandan Boko Haram, Abu Usamah

Zaratan dakarun rundunar Sojin Najeriya dake aikin Operation Lafiya Dole sun samu nasarar halaka wani babban kwamandan kungiyar ta’addanci na Boko Haram, Abu Usamah tare da gomman mayakan ta’addanci.

Daily Nigerian ta ruwaito shugaban sashin watsa labaru na rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, inda yace Sojojin sun samu wannan nasara ne a karan battan da suka yi da Boko Haram a Gorgi, karamar hukumar Damboa.

KU KARANTA: Annobar Corona: Aminu Dantata ta bayar da naira miliyan 300 domin yaki da Corona

A cewar Onyeuko, wannan nasara da rundunar Sojin Najeriya ta samu ya samar da wata babbar gibi a shugabancin kungiyar Boko Haram, ya kara cewa sun kwato bindigar AK-47 guda 2, albruusai, bindigar harba Bom da sauran ababe da dama.

“Wani sadarwa da muka tatsa kuma binciken kwakwaf ya tabbatar mana da sahihancinsa ya nuna cewa Abu Usamah na daga cikin yan ta’addan da Sojojinmu suka kashe a musayar wutar da muka yi a Gorgi.

“Ya samu raunin harbin bindiga a yayin da ake barin wuta, don haka mayakansa suka gaggauta dauke shi daga filin daga, amma duk da haka daga bisani ya mutu, mutuwarsa ta samar da babban gibi a shugabancin Boko Haram.

“Kuma dakarunmu za su cigaba da dagewa wajen tabbatar da sun gama da kakkabin yan Boko Haram da suka rage a mabuyansu dake yankin Arewa maso gabas.” Inji shi.

A wani labari kuma, Sojojin rundunar Task Force ta 159 dake garin Kanama cikin karamar hukumar Yunusari sun kashe mayakan Boko Haram da na ISWAP yayin da suka yi kokarin kutsa kai cikin sansaninsu a ranar Juma’a.

Sojojin sun samu nasarar kashe yan ta’addan ne da goyon bayan dakarun rundunar Sojin sama, inda suka tafka ma kungiyoyin ta’addancin mummunar barna a bangaren mayaka da kuma kayan aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel