Gwamna Zulum ya garkame Borno, yace Coronavirus ta fi karfin Boko Haram

Gwamna Zulum ya garkame Borno, yace Coronavirus ta fi karfin Boko Haram

Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar da sanya dokar ta-baci a duk fadin jahar sa’annan ya bayyana musu cewa Coronavirus ya fi karfin ta’addancin Boko Haram.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Zulum ya bayyana haka ne cikin wani sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, inda yace annobar Corona ta zama wata sabuwar jarrabi ga jama’an jahar, don haka akwai bukatar daukan mataki.

KU KARANTA: Annobar Corona: Aminu Dantata ta bayar da naira miliyan 300 domin yaki da Corona

“A wannan lokaci muna fama da wani lamari mafi hadari a sakamakon COVID-19 wanda yake ta yaduwa a duk fadin duniya ba tare an gano maganinsa ba, hanya mafi inganci na yaki da wannan cuta shi ne samar da wata dabara na kare yaduwarsa.

“Gwamnatin tarayya ta samar da hanyoyin kariya daban daban a duk fadin kasar, musamman a Abuja da Legas wanda suka fi yawan mutanen dake dauke da cutar domin kare yaduwarsa, gwamnatocin jahohi da dama sun samar da irin nasu tsare tsare na tabbatar da cutar bata shiga jahohinsu ba” Inji shi.

Don haka yace gwamnatin jahar Borno ta yanke shawarar samar da sabbin tsare tsaren yaki da yaduwar da cutar bisa shawarar kwamitin kula da yaki da Coronavirus a karkashin jagorancin mataimakin gwamna.

Daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka, kuma Gwamna Zulum ya bayyana akwai dakatar da ma’aikata daga mataki na 12 zuwa zuwa wajen aiki, tabbatar da dukkanin shaguna sun samar da ababen wanke hannu, tare da tabbatar an tsaya nesa nesa da juna.

“Dukkanin bankuna dole ne su samar da kayan wanke hannu, kuma ba zasu bari mutane fiye da 15 su shiga cikin banki a lokaci daya ba, haka zalika dole ne ya kasance akwai kudi a na’urar ATM na tsawon awa 24.

“Motocin haya na Bus zasu koma daukan mutane 3 a kowanne kujera, mutane biyu kuma a keke napep. An dakatar da shigowar motoci ko fita daga jahar, banda motocin abinci, magunguna, man fetir da kayan jin kai. Haka zalika makarantu za su cigaba da zama a rufe.” Inji shi.

Daga karshe ya nemi jama’a su dage da gudanar da addu’o’i don neman agajin Allah madaukakon Sarkin game da wannan jarrabi da aka tsinci kai a ciki, ko Allah Ya kawo mana sauki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel