Ku barni na dauki diyata ta mutu a gabana - Magidanci ya nemi gwamnati ta bashi 'yarshi bayan yaga wajen da ake kula da su bai da kyau

Ku barni na dauki diyata ta mutu a gabana - Magidanci ya nemi gwamnati ta bashi 'yarshi bayan yaga wajen da ake kula da su bai da kyau

- Wani fusataccen mahaifin ya bayyana halin da diyar shi ke ciki a wata cibiyar killace masu cutuka masu yaduwa

- Duk da dattijon bai sanar da sunan wacce cibiyar bace, ya ce tunda aka kai diyar shi sun ki kulata duk da an gano tana dauke da Coronavirus

- A cewar mahaifin, hatta abinci an hana ta kuma babu likita ko ma'aikaciyar jinyar da ta duba ta tun zuwansu sai cewa da ake musu su tafi gida

Wani bidiyon dattijon mutum wanda aka gano mahaifin wata yarinya ce da aka killace a cibiyar killace cutuka masu yaduwa ya mamaye yanar gizo.

An ga dattijon na korafi cike da kunar rai a kan halin da diyar shi ke ciki.

Mutumin da ya bayyana sunan shi da Olanutu, ya sanar da manema labarai ne yayin da ake tattaunawa da shi cewa an gano diyar shi na dauke da cutar coronavirus. An kuma bar ta ba a kula da ita a daya daga cikin cibiyoyin killace masu jinyar cutuka masu yaduwa kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

KU KARANTA: Allah Sarki: Yadda Almajiri ya mutu a ruwa a yayin da yake kokarin boyewa masu kamen hana fita a Kaduna

Duk da bai bayyana sunan cibiyar ba, fusataccen mahaifin ya ce an bar diyar shi babu abinci tun bayan da aka kawo ta cibiyar.

"Ministar ta zo da kanta ta ga abinda yake faruwa. Ba karya nake yi ba. Sunana Olanutu. Me suke yi a nan? Tun safe bata ga likita ba ko ma'aikaciyar jinya. Ba a ciyar da ita ba kuma suna cewa in dauketa. Bari muje gida kawai ta mutu a can tunda babu wanda ya damu da ita. Idan tana dauke da cutar ba yana nufin ta samu lasisin mutuwa bane" ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng