Allah Sarki: Yadda Almajiri ya mutu a ruwa a yayin da yake kokarin boyewa masu kamen hana fita a Kaduna

Allah Sarki: Yadda Almajiri ya mutu a ruwa a yayin da yake kokarin boyewa masu kamen hana fita a Kaduna

- Wani almajiri ya halaka sakamakon ruwan da ya tafi dashi bayan malamin shi ya boye shi a Kaduna

- Kamar yadda kwamishinan kula da walwala ta jihar, Hafsat Baba ta bayyana, malamin yaron ya boye shi ne duk da gwamnatin jihar Kaduna ta kwashe almajiran don komawa gida

- Ta ce za a hukunta malamin duk da a halin yanzu yana hannun jami'an tsaro don kowanne rai na da matukar amfani a jihar

Wani almajiri ya halaka bayan ruwa ya tafi dashi a yayin da yake boyewa gwamnatin jihar Kaduna da ta bada umarnin kwashe almajirai daga jihar a matsayin hanyar hana yaduwar cutar coronavirus a jihar.

An gano cewa malamin almajirin mai suna Malam Umar Musa Mai kalanzir ne ya boye shi a wajen bakin ruwa da ke Kabala West ta karamar hukumar Kaduna ta Kudu. A nan ne kuwa ya hadu da ajalin shi.

Allah Sarki: Yadda Almajiri ya mutu a ruwa a yayin da yake kokarin boyewa masu kamen hana fita a Kaduna

Allah Sarki: Yadda Almajiri ya mutu a ruwa a yayin da yake kokarin boyewa masu kamen hana fita a Kaduna
Source: UGC

Bayan barkewar annobar Coronavirus ne gwamnatin jihar ta bayyana rufe duk makarantu wadanda suka hada da na tsangaya tare da umartar dukkan almajirai da su koma gaban iyayensu.

Wannan ci gaban kuwa ya kawo kwashe almajirai 20,731 daga garin Kaduna a ranar 30 ga watan Maris din 2020.

A yayin martani a kan mutuwar da almajirin yayi a cikin ruwa, Kwamishin ma'aikatar walwala ta jihar Kaduna, Hafsat Baba, ta nuna damuwarta a kan mutuwar almajirin.

Ta jajanta yadda wasu malaman suka ki bin dokar gwamnatin jihar.

"Don gujewa biyayya ga umarnin gwamnatin jihar, wasu malaman sun boye daliban don kada a mayar dasu kauyukansu." Ta ce.

"Gwamnatin jihar Kaduna ta zargi hakan zai iya zama hatsari ga yaran kuma tuni ta nemo salon tseratar dasu.

Alaramma Umar Musa mai Kalanzir ya yi ikirarin cewa ya mayar da dukkan dalibansa hannun iyayensu, amma sai ga wannan mummunan lamarin ya faru.

Yayin tabbatar da cewa za a hukunta malamin, ta kara da cewa tuni jami'an tsaro suka damke malamin kuma ana ci gaba da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel