An cire dokar hana yara mata masu ciki zuwa makaranta a kasar Sierra-Leone

An cire dokar hana yara mata masu ciki zuwa makaranta a kasar Sierra-Leone

- A ranar Litinin, 30 ga watan Maris ne gwamnatin kasar Sierra Leone ta janye dokar hana yara mata masu juna biyu zuwa makaranta

- Tun a 2015 gwamnatin kasar Sierra Leone ta saka dokar hana yara mata masu juna biyu zuwa makaranta

- Amma kuma bayan fafatawa da aka yi da gwamnatin kasar da kungiyar kare hakkin dan Adam a kotu, kungiyar tayi nasara inda aka janye dokar

Kasar Sierra Leone a ranar Litinin ta dage dokar hana yara mata masu juna biyu halartar makaranta. Wannan dokar an dage ta ne a ranar Litinin 30 ga watan Maris bayan fafutukar masu rajin kare hakkin dan Adam wanda ya dauka shekaru biyar.

Wannan dokar kuwa an samar da ita ne a shekarar 2015 bayan hauhawar fyade, cin zarafi da talauci yayin barkewar annobar Ebola wacce ta kawo hauhawar ciki ga yara mata masu karancin shekaru.

An cire dokar hana yara mata masu ciki zuwa makaranta a kasar Sierra-Leone
An cire dokar hana yara mata masu ciki zuwa makaranta a kasar Sierra-Leone
Asali: Getty Images

A yayin da gwamnatin kasar ta jaddada cewa yara mata masu juna biyu ba za su halarci makarantu ba, ta sa ana tsangwamarsu sannan ana kyamarsu a cikin jama'a.

A takardar da ke bayyana janye dokar, an bayyana cewa ma'aikatar ilimin firamare da sakandire tana sanar da dage dokar hana yara mata masu juna biyu halartar makarantu.

"Janye dokar mataki ce na farko da ke bayyana kokarin gwamnatin kasar Sierra Leone na samar da ingantaccen ilimi ga yara."

Ministan ilimi, David Sengeh ya ci gaba da bayyana cewa dage dokar za a maye gurbinta da sabbin dokoki biyu.

Judy Gitau, shugaban kungiyar rajin kare hakkin mata ta Afrika mai suna women's Rights group Equality Now, wacce ke aiki da gwamnati, ta ce dokokin tsaron za su hada da bada kariya ga mata daga cin zarafi a makarantu.

Jaridar Reuters ta ruwaito cewa kungiyar kare hakkin dan Adam din ta maka gwamnatin kasar Sierra Leone din a babbar kotun yammacin Afrika a 2018. A watan Disamba ne kotun ta yanke hukunci inda ta bi bayan kungiyar. Ta ce dokar kasar ta bayyana wariya tare da cin zarafi a kan hakkin yara mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng