Sarki mai daraja ta daya a Najeriya ya bayyana tsirrai 2 da ke maganin cutar coronavirus

Sarki mai daraja ta daya a Najeriya ya bayyana tsirrai 2 da ke maganin cutar coronavirus

A jiya, Litinin, ne Babban sarki mai daraja ta daya a Najeriya, Ooni na Ife, Enitan Ogunwusi, ya bayyana wasu tsirrai guda biyu da ya yi ikirarin cewa suna maganin kwayar cutar coronavirus.

Muguwar cutar coronavirus ta hallaka mutane fiye da 30,000 a duniya a cikin watanni uku kacal.

Yanzu haka akwai mutane fiye da 100 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar coronavirus a Najeriya. An sallami mutane 8 daga cibiyar killacewa bayan an tabbatar cewa sun warke daga muguwar cutar covid-19.

A cewar basaraken, tun a ranar 6 ga watan Yuni na shekarar 2019 aka saukar da wahayi a kan maganin cutar covid-19, lokacin bikin al'ada na Ifa mai taken 'Otura Meji'.

Mai martarba Ogunwusi ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta (tuwita).

Sarki mai daraja ta daya a Najeriya ya bayyana tsirrai 2 da ke maganin cutar coronavirus
Ooni na Ife
Source: Depositphotos

"Mun sanar da jama'a tuntuni a kan ballewar wata annoba da ba a ganinta, amma tsirari ne daga cikin mutane suka saurare mu," a cewar basaraken.

Sannan ya cigaba da cewa, "Jama'a su sani cewa an ambaci tsirran 'Efod/Urim' da 'Thurim' a cikin littafi mai tsarki. Daya suke da tsirranmu na gargajiya da basu taba bamu kunya ba. Na yi aiki da kasashen duniya da dama, musamman kasar Cuba, a kan tasirin wadannan tsirrai.

DUBA WANNAN: Yadda cutar coronavirus ta hallaka matashin dalibi dan Najeriya da ke karatu a Amurka

"Karni da dama suka gabata, kasar Cuba ta dogara ne da dabarun magabata da tsirrai, hakan ne yasa suke sahun gaba a bangaren harkar kiwon lafiya a duniya. Cuba ce kadai kasar da take taimakon duniya."

Babban basaraken ya bayyana cewa ubangiji ya girmi duk wani addini, a saboda haka ya kamata duniya duniya baki daya ta mika wuya tare da rungumar abubuwan da ubangiji ya samar.

"Matukar ana son warware annobar wannan cuta, da wadannan tsirrai da ubangiji ya samar za a yi amfani. Na yi amfani da su a kan wadanda cutar coronavirus ta kwantar, kuma sun bayar da shaida bayan sun warke," a cewarsa.

Ya kalubalanci masu bincike a bangaren kimiyya a gida Najeriya da duniya baki daya a kan su gwada wadannan tsirrai a kan masu dauke da cutar corona tare da samar da rigakafi daga tsirran.

Sarkin ya bayyana shirinsa na yin aiki tare da masana domin basu duk gudunmawar da suke bukata wajen samun tsirran da kuma yadda ake sarrafa su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel