Covid-19: Gwamna Umahi ya bayar da umurnin bindige duk wanda ya yi yunkurin tserewa daga asibiti

Covid-19: Gwamna Umahi ya bayar da umurnin bindige duk wanda ya yi yunkurin tserewa daga asibiti

Gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi, a jiya Litinin, 30 ga watan Maris, ya umurci jami’an tsaro da su bindige duk wanda ya dawo jahar sannan ya yi kokarin guduwa daga inda ake killace mutane.

Gwamnatin jahar a karshen makon da ya gabata ta yi umurnin gaggawan killace akalla mutane 37 da suka shigo jahar ta daji bayan gwamnatin jahar ta yi umurnin rufe iyakokinta.

Gwamnatin jahar ta yi umurnin cewa a gaggauta rufe dukkanin iyakoki a jahar domin hana yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

Gwamnan ya kara da cewar a bindige duk wani bako da ya dawo sannan ya yi kokarin guduwa daga cibiyar killace mutane wanda a nan ne za a dunga yi musu gwaji a kullun har tsawon kwanaki 14 biyo bayan barkewar annobar coronavirus.

Covid-19: Gwamna Umahi ya bayar da umurnin bindige duk wanda ya yi yunkurin tserewa daga asibiti
Covid-19: Gwamna Umahi ya bayar da umurnin bindige duk wanda ya yi yunkurin tserewa daga asibiti
Asali: Twitter

Amma akalla mutane 30 ne aka ce sun shiga jahar ta jeji sannan suka tsallake garin da ke iyaka a tsakanin Abakaliki da Enugu inda dama aka riga aka ajiye ababen hawa da zai kwashe su zuwa wuraren da za su.

Daga bisani sai aka kwashi mutanen su 30 da suka tsere da wasu bakwai da suka dawo zuwa cibiyar killacewa a filin wasa na Abakaliki inda Umayi ya ziyarce su da karfe 9:00 na dare sannan ya yi umurnin cewa a dunga gwada su a kullun har tsawon kwanaki 14.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Yadda titunan Abuja suka zama tamkar kufai (hotuna)

A wani labarin kuma mun ji cewa Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya ci karo da wata katuwar mota da ta nemi shigowa jihar Kano bayan an rufe iyakokin shiga jihar.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi ram da wannan mota ne sa’ilin da ya fito wani kewaye a Ranar Litinin, 30 ga Watan Maris, 2020, kamar yadda mu ka ji labari.

Darektan harkokin yada labarai na gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakassai ne ya bayyana wannan a shafinsa na Tuwita, inda ya wallafa bidiyon haduwar.

Wannan gingimari wanda ta ke cike da jama’a ta yi kokarin shigowa cikin Kano ne duk da gwamnatin jihar ta garkame iyakokinta saboda annobar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel