Gwamnan Kano ya kama motar da ta shigo Kano bayan rufe iyakoki saboda annoba

Gwamnan Kano ya kama motar da ta shigo Kano bayan rufe iyakoki saboda annoba

Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya ci karo da wata katuwar mota da ta nemi shigowa jihar Kano bayan an rufe iyakokin shiga jihar.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi ram da wannan mota ne sa’ilin da ya fito wani kewaye a Ranar Litinin, 30 ga Watan Maris, 2020, kamar yadda mu ka ji labari.

Darektan harkokin yada labarai na gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakassai ne ya bayyana wannan a shafinsa na Tuwita, inda ya wallafa bidiyon haduwar.

Wannan gingimari wanda ta ke cike da jama’a ta yi kokarin shigowa cikin Kano ne duk da gwamnatin jihar ta garkame iyakokinta saboda annobar COVID-19.

Salihu Tanko Yakassai ya bayyana cewa Tawagar gwamnan ta raka wadannan mutane da aka kama zuwa ofishin ‘Yan Sandan da ya fi kusa domin a hukuntasu.

KU KARANTA: COVID-19: Ganduje ya koka da rashin tsaro a bakin iyakoki

A wannan bidiyo an ji Mai girma gwamna Abdullahi Ganduje ya na tsawatawa Direban motar yayin da wadanda aka dauko a motar su kayi ta yi wa gwamnan shewa.

Direban wannan mota ya fadawa gwamnan Kano cewa sun fito ne daga Garin Madalla da ke cikin karamar hukumar Suleja a Neja, kusa da babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan da Tawagarsa su na sanye da safar hannu domin gudun kamuwa da cutar Coronavirus. Sai dai da alamu gwamnan bai rufe fuskarsa da tsummar kariya ba.

Kawo yanzu babu wanda ya kamu da wannan cuta ta COVID-19 a jihar Kano mai tarin jama’a. Gwamnatin Ganduje ta na cigaba da kokarin kare rayukan al’umma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel