Dokar hana zirga-zirga a Kaduna: 'Yan sanda sun kama mutane 165 sun kuma kwace ababen hawa 205
- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama mutane 165 da kuma ababen hawa 205 sakamakon kin bin dokar ta-bacin da gwamnatin jihar ta saka
- Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya bayyana, rundunar 'yan sandan da sauran cibiyoyin tsaro sun hada kai don tabbatar da jama'a sun bi dokar
- A cikin mutane 165 da aka damke, akwai wasu malamai biyu wadanda suka ki bin dokar hana taro suka ja sallar jam'i a Unguwar Kanawa da ke Kaduna
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama mutane 165 da kuma ababen hawa 205 sakamakon karya dokar ta-bacin da aka saka a jihar don hana yaduwar cutar COVID-19.

Asali: UGC
Wannan na kunshe ne a takardar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ya fitar a ranar Litinin.
Kamar yadda takardar ta bayyana, "Biyo bayan dokar ta bacin da aka saka a jihar Kaduna a ranar 27 ga watan Maris 2020 da kuma dokar gwamnatin tarayya ta nisantar taruka don hana yaduwar cutar coronavirus, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna karkashin jagorancin Kwamishinan 'yan sanda U.M Muri, tare da hadin guiwar sauran cibiyoyin tsaro, suna tabbatar da cewa an bi dokar.
"Jami'an rundunar tare da sauran hukumomin tsaro sun kama mutane 165 tare da ababen hawa 205 da suka hada da motoci da babura. Akwai malaman addini biyu da aka damke bayan sun ki bin dokar hana taro."
Ya yi kira ga jama'a da su kasance masu bin doka, kiyaye dokokin hana yaduwar cutar da kuma ci gaba da zama a gida don tabbatar da lafiyar jama'ar jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng