N10,000 muke kashewa wajen gudanar da gwajin Coronavirus a kan duk mutum 1 – Gwamnati

N10,000 muke kashewa wajen gudanar da gwajin Coronavirus a kan duk mutum 1 – Gwamnati

Karamin ministan kiwon lafiya, Dakta Olurunnimbe Mamore ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na kashe kimanin naira dubu 10 wajen gudanar da gwajin Coronavirus ta hanyar amfani da tsarin hukumar kiwon lafiya ta Duniya, WHO, dake bayar da gamsashshen sakamako.

Jaridar Sun ta bayyana Mamora ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake ganawa da yan jaridu a babban birnin tarayya Abuja, inda yace amma gwamnati ba wai ta damu da kashe kudin bane, tunda dai ana samun sahihin sakamako.

KU KARANTA: Annobar Corona: Aminu Dantata ta bayar da naira miliyan 300 domin yaki da Corona

Da wannan ne tasa gwamnati ta dage a kan lallai ba za’a gudanar da gwajin Coronavirus a Najeriya ba sai an samu ingantattun kayan aikin yin gwajin kamar tadda hukumar WHO ta bukata.

“Bani da takamaimen farashin a kai na, amma dai na san gwamnati na kashe kimanin N10,000 don gudanar da gwajin Coronavirus, toh ko a N10,000 ka duba makudan kudaden da za’a kashe duba da yawan jama’an dake bukatar a gwada su.

“Watakila hakan ne yasa wasu ke ganin ya kamata mu sauya tsarin yin gwajin, amma ba zamu yarda da hakan ba saboda hukumar kiwon lafiya a duniya, WHO ba ta amince da hakan ba, WHO ta amince da tsarin PCR ne kawai don samun sahihin sakamako.

“Haka zalika ba wai kawai maganan a sayo injin gwaji bane, a’a, akwai maganan kwararrun ma’aikata, saboda injinoni ne na zamani dake bukatar kwararru da suka samu horo sosai wajen iya amfani da su domin a samu sahihin sakamako.” Inji shi.

A wani labarin kuma, a kokarinta na rangwanta ma al’ummar Najeriya bisa mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki sakamakon barkewar annaobar Coronavirus, gwamnatin Najeriya ta nemi kamfanonin sadarwa su sassauta ma yan Najeriya.

Gwamnatin ta bayyana haka ne ta bakin Ministan sadarwa, Sheikh Dakta Isah Ali Pantami, wanda ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sadarwar zamani ta Facebook a daren Talata, inda ya umarci kamfanonin su rage farashi kira da na Data don saukaka ma yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel