COVID-19: Mun fara aika wa talakawa tallafin kudi - Ministar Buhari
Sadiya Farouk, ministar walwala da jin dadin 'yan kasa, ta ce ma'aikatarta ta fara tura kudi ga gidaje masu matukar talauci a fadin kasar nan don rage musu radadin takurar bullowar cutar coronavirus.
Ministar ta sanar da hakan ne a yayin jawabi ga manema labarai a Abuja, a ranar Litinin.
Farouk ta ce ma'aikatarta ta fara biyan gidajen da aka sani cewa suna fama da tsananin talauci kuma ake tallafa musu har da basu albashi kowanne wata.
Ta ce sauran rukunin jama'ar da za a tallafawa sun hada da karin matalauta a yayin da ake fama da annobar cutar corona mai sarke numfashi.
"A sakin layi na 54 a cikin jawabin shugaban kasa, ya umarceni da na fara biyan albashin watanni biyu. Mun kuwa yi hakan. Mun yi umarnin cewa a fara biyan matalauta kudin a fadin kasar nan," a cewarta.
Sannan ta cigaba da cewa, "saboda cutar coronavirus, akwai wasu rukunin mutane da za a fara basu tallafi saboda gwamnati ta san cewa kullum sai sun fita suke nemo abinda za su ci. Muna duba yadda za a mika musu kayan abinci tare da kayayyakin da za su rage musu damuwa a wannan lokaci na tsanani."
DUBA WANNAN: Annobar coronavirus: Gwamnatin tarayya ta shigar da karar wasu manyan shaguna 4 saboda kara farashin kaya
Ministar ta ce hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta tura manyan motoci dauke da kayan tallafi ga jama'a a jihohin da aka tabbatar da barkewar cutarv coronavirus.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng