An tura fasto gidan yari saboda karyata cutar coronavirus
Hukumomi a kasar Uganda sun damke tare da tura wani fasto gidan yari bayan ya musanta wanzuwar cutar coronavirus a nahiyar Afirka.
Babban faston mai suna Augustine Yiga, an zargesa ne da sanar da mabiyansa cewa babu wata coronavirus a Uganda da nahiyar Afirka.
"Fasto Yiga na cocin Revival Christian an gurfanar dashi tare da tura shi gidan yari sakamakon yunkurin assasa yaduwar muguwar cutar coronavirus a kasar," mai magana da yawun 'yan sandan kasar Uganda, Patrick Onyango ya sanar.
"Ikirarin cewa babu coronavirus a Afirka da Uganda na nuna zagon kasa ga kokarin gwamnati na yakar cutar tare da hurewa jama'a kunne don su samu cutar," ya kara da cewa.
Amma kuma lauyan faston mai suna Wilberforce Kayiwa, ya ce Yiga ya musanta zarginsa da aka yi da kokarin yada kwayar cutar. A halin yanzu an yankewa faston shekaru 7 a gidan yari.
Yiga, wanda ya mallaki gidan talabijin da rediyon don wa'azi, yana da mutane masu yawa da ke binsa kuma kwararre ne a wajen akidu mabanbanta da ikirarin manzonci.
DUBA WANNAN: Jagorantar Sallar Juma'a: Sheikh Jingir ya saduda bayan ya amsa gayyatar DSS
A halin yanzu dai, kasar Uganda na da mutane 33 da suka kamu da cutar.
Shugaban kasa Yoweri Museveni yayi kira ga jama'a da su zauna a gida amma kuma bai rufe kasar ba.
Tun wata daya da ya gabata aka rufe makarantu, wuraren nishadi, wuraren bauta da kuma kasuwanni. An hana jama'a hawa abun hawa na haya tare da zuba mutane fiye da uku a motar gida.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng