Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 20 sun kamu da cutar Coronavirus, Legas Abuja da Kaduna
Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane ashirin da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya.
Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Litinin inda tace: “An tabbatar da mutane ashirin sun kamu da #COVID19 a Najerya. 13 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Kaduna, .“
“Dai-dai Karfe 9:o0 na daren 30 ga Maris, mutane 131 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami takwas, kuma biyu ya rigamu gidan gaskiya.“
Ga jerin jiha-jiha
Lagos- 81
FCT- 25
Ogun- 3
Enugu- 2
Ekiti- 1
Oyo- 8
Edo- 2
Bauchi- 2
Osun-2
Rivers-1
Benue- 1
Kaduna- 3

Asali: Twitter
Mun kawo muku rahoton cewa Uwargidar Malam Nasir El-Rufai, Hadiza Isma-El-Rufai ta shaidawa Duniya cewa ta ta yi gwajin wannan cuta mai yawo. Amma ba a ji labarin sakamakon ba tukuna.
Hajiya Hadiza Isma-El-Rufai ta yi wannan bayani ne a shafinta na sada zumunta na Tuwita. Mai dakin gwamnan ta kuma godewa addu’o’in da jama’a su ke yi masu.
Hadiza El-Rufai ta nuna cewa Gwawnan ya na ta fama da zaman kadaici na kebewa sauran jama’a, domin gudun yada wannan mummunar cuta ga sauran Bayin Allah.
Isma-El-Rufai ta ce: “Nagode Jama’an Tuwita da duka addu’o’i da fatan alherinku. Mai girma gwamna ya na samun lafiya.”
Har yanzu cutar ba ta fara bayyana a jikinsa ba. Daga baya yau za a yi mani gwaji. Ina sa ran ganin alheri. A halin yanzu mu na cigaba da zaman kebewa jama’a.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng