Hadiza Isma-El-Rufai ta na jiran sakamakon gwajin cutar COVID-19

Hadiza Isma-El-Rufai ta na jiran sakamakon gwajin cutar COVID-19

Yayin da aka tabbatar da cewa Mai girma gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya na dauke da kwayar cutar Coronavirus, mai dakinsa ta ce ta yi gwajin wannan cuta.

Uwargidar Malam Nasir El-Rufai, Hadiza Isma-El-Rufai ta shaidawa Duniya cewa ta ta yi gwajin wannan cuta mai yawo. Amma ba a ji labarin sakamakon ba tukuna.

Hajiya Hadiza Isma-El-Rufai ta yi wannan bayani ne a shafinta na sada zumunta na Tuwita. Mai dakin gwamnan ta kuma godewa addu’o’in da jama’a su ke yi masu.

Hadiza El-Rufai ta nuna cewa Gwawnan ya na ta fama da zaman kadaici na kebewa sauran jama’a, domin gudun yada wannan mummunar cuta ga sauran Bayin Allah.

Isma-El-Rufai ta ce: “Nagode Jama’an Tuwita da duka addu’o’i da fatan alherinku. Mai girma gwamna ya na samun lafiya.” Mai dakin Gwamnan ta kara da cewa:

KU KARANTA: Za a rika yin gwajin cutar COVID-19 a Kaduna, Sokoto da Kano

“Har yanzu cutar ba ta fara bayyana a jikinsa ba. Daga baya yau za a yi mani gwaji. Ina sa ran ganin alheri. A halin yanzu mu na cigaba da zaman kebewa jama’a.”

Matar gwamna El-Rufai ta yi wannan jawabi ne Ranar Lahadi da kusan karfe 9:00 na safe. Wannan ya zo ne kwana guda bayan an ji cewa Mai gidanta ya kamu.

Hajiya El-Rufai wanda ta ke da tarin Mabiya a shafin Tuwita ta bukaci a taya su da addu’a tun bayan da labari ya zo mata cewa Mai gidanta ya na dauke da COVID-19.

Da ta ke wani bayani a karshen makon jiya, Hadiza Isma-El-Rufai ta bayyana cewa ba ta taba sanin irin tarin amfanin gwiwar hannu ba sai dai cutar COVID-19 ta bullo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel