Gwaji ya nuna Gwamna Seyi Makinde ya na dauke da kwayar COVID-19

Gwaji ya nuna Gwamna Seyi Makinde ya na dauke da kwayar COVID-19

Mai girma gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde ya kamu da cutar Coronavirus. Gwamnan ya tabbatar da wannan da kansa a yau Litinin, 29 ga Watan Maris.

Oluwaseyi Makinde ya bada wannan sanarwa ne ta shafinsa na Tuwita watau @SeyiMakinde. Gwamnan ya ce gwaji ya nuna cewa ya na dauke da wannan cuta.

Makinde yake cewa: “Yanzu na samu labarin gwajin cutar COVID-19 da na yi. Ina dauke da cutar. Alamomin ciwon ba su fara bayyana a kai na tukuna ba tukuna.”

Injiniya Makinde ya kuma kara da cewa: “Zan cigaba da kebe kai na daga bainar jama’a.” Gwamnan ya bayyana wannan ne da karfe 6:04 na yamman Litinin.

Gwamnan ya bayyana cewa ya nada tsohon shugaban asibitin koyar da aiki na jami’ar Ibadan, Temitope Alonge a matsayin shugaban kwamitin yaki da cutar a Oyo.

KU KARANTA: Jihar Adamawa ta sa dokar ta-baci saboda annobar COVID-19

Farfesa Temitope Alonge shi ne zai jagoranci wannan kwamiti da za su yi aikin ganin bayan annobar Coronavirus, yayin da gwamnan ya ke faman jinya a jihar.

A jawabin gwamna Seyi Makinde, ya yi kira ga mutanensa su cigaba da bin sharudan da aka kafa na cewa kowa ya tsaya a cikin gida, domin a rage yaduwar annobar.

A halin yanzu masu dauke da wannan cuta a Najeriya sun haura mutane 100. Rahotannin da mu ka samu daga hukumar NCDC shi ne cutar ta kashe mutane biyu yanzu.

Da wannan sakamako da aka bayyana da yamman nan, gwamnonin da ke dauke da COVID-19 a kasar nan sun zama uku, bayan Nasir El-Rufai da kuma Bala Mohammed.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel