Manyan yan Najeriya 11 da suka bayar da gudunmawar kudi domin yakar coronavirus

Manyan yan Najeriya 11 da suka bayar da gudunmawar kudi domin yakar coronavirus

Yayinda Najeriya ke yaki da hana yaduwar cutar Coronavirus, wasu manyan masu kudi da kamfanoni sun bayar da tallafin kudade domin taimakawa gwamnatoci a matakan tarayya da jaha.

Hakan ya sa Legit.ng ta zakulo manyan yan Najeriya 11 da suka ba gwamnati kyautar kudade domin hana yaduwar cutar Coronavirus a kasar.

1. Aliko Dangote

Da farkon shigowar annobar Najeriya,shugaban gidauniyar Dangote, Aliko Dangote ya bayar da gudanarwa naira miliyan 200 ga gwamnatin a madadin gidauniyarsa.

Dangote ya zo ya kara kudin zuwa naira biliyan daya sannan ya hada hannu da wani babban banki wajen samar da cibiyar kula da killace masu cutar.

Ya kuma bayar da gudanarwa motocin daukar marasa lafiya ga gwamnatin jahar Lagas.

Manyan yan Najeriya 11 da suka bayar da gudunmawar kudi domin yakar coronavirus
Manyan yan Najeriya 11 da suka bayar da gudunmawar kudi domin yakar coronavirus
Asali: UGC

2. Femi Otedola

Ya ba gwamnati gudanarwa naira biliyan daya domin yakar cutar ta Covid-19.

KU KARANTA KUMA: Labari da dumi-dumi: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus

3. Tony Elumelu

A madadin bankin United Bank of Africa (UBA) ya bayar da naira biliyan daya ga gwamnatin jahar Lagas.

4. Abdulsamad Rabiu

Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ya sanar da bayar da kyautar naira biliyan daya ga gwamnati.

5. Modupe da Folorunasho Alakija

Shugaba da mataimakiyar Shugaban Famfa Oil Limited sun bayar da naira biliyan daya.

6. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa ma ya bayar da naira biliyan 50.

7. Asiwaju Bola Tinubu

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu ya sanar da bayar da naira miliyan 200.

8. Herbert Wigwe

Shugaban bankin Access ya bayar da naira biliyan daya.

9. Segun Agbaje

Manajan darakta na bankin Guaranty Trust Bank ma ya bayar da naira biyan daya a madadin bankin.

10. Mike Adenuga

Mike Adenuga, wanda shima biloniyan Najeriya ne ya bayar da naira biliyan 1.5.

11. Innocent Ujah Idibia

Mawakin Najeriya da aka fi sani da TuBaba shima ya bayar da naira miliyan 10 domin yakar cutar ta oronavirus a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel