Labari da dumi-dumi: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus

Labari da dumi-dumi: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar coronavirus a kasar.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya sanar da hakan a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, a lokacin taron tawagar fadar Shugaban kasa kan cutar Covid-19 a Abuja, babbar birnin kasar, Channels TV ta ruwaito.

Ya ce: “Zuwa yanzu, an salami mutum uku bayan sun warke. Amma abun bakin ciki, an kara rasa rai a karshen mako sakamakon mummunan yanayi na rashin lafiya da mara lafiyan ya shiga.

Labari da dumi-dumi: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus

Labari da dumi-dumi: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus
Source: UGC

“Mun jajirce wajen gano wadanda suka yi tarayya kuma manufamu shine hanyar shawo kan lamarin cikin gaggawa, killace su da kuma bibiyar wadanda suka yi tarayya dasu sannan suma a killace su da kuma yi masu magani, domin rage yaduwar cutar.”

“A yau 30 ga watan Maris, 2020, mun samu mutane 111 da aka tabbatar suna dauke da Covid-19 a Najeriya wadanda 68 suka kasance a Lagas, 21 a babbar birnin tarayya, bakwai a Oyo, uku a Ogun, biyu a Bauchi,biyu a Edo, biyu a Osun, biyu a Enugu, sannan daddaya a Benue, Ekiti, da Rivers."

Ya kara da cewa Najeriya ta tabbatar da masu coronavirus 111, cewa mafi akasarinsu wadanda suka dawo daga kasashen waje ne.

A cewar ministan lafiyan, an fi samun yawan wadanda suka kamu a Lagas da Abuja ne saboda sune ,manyan kofofin shigowa kasar.

Ehanire ya gargadi yan Najeriya da su kare tsoffi a cikinsu, da wadanda ke fama da lalura ta rashin lafiya domin sune suke cikin mafi hatsari.

A baya mun ji cewa gwamnatin jihar Legas ta sallam wasu mutane biyar daga cibiyar killacewa da ke asibitin cututtuka masu yaduwa a unguwar Yaba bayan an tabbatar da cewa yanzu basa dauke da kwayar cutar coronavirus.

Ya zuwa yanzu an sallami jimillar mutane 8 kenan daga cibiyar.

Mutanen da aka sallama suna cikin koshin lafiya, babu alamar gajiya ko damuwa a tare da su, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel