Jahilci ne: Kungiyar JNI ta sarkin Musulmi ta yi raddi ga malaman da suka karyata cutar coronavirus
Kungiyar jama'atu Nasrul Islam wacce ke karkashin jagorancin Sarkin Musulmai ta bayyana cewa jahilci ne wani malamin addini ya danganta cutar coronavirus da karya.
Kungiyar ta bada wannan sanarwar ne a ranar Litinin wacce ke dauke da jan kunne ga malaman. Ta ce suna dulmiyar da jama'a ne a kan cutar Coronavirus a Najeriya.
Sanarwar da ta zama martani ga wasu rukunin malaman addinin Musulunci da suka fito suna wa'azi ga mabiyansu tare da danganta cutar coronavirus da makircin yahudawa.
A sanarwar JNI din, sakataren kungiyar, Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya ce bai kamata wadannan kalaman na fitowa daga bakin duk wani malamin da ya amsa sunansa ba.
Kungiyar ta bayyana takaicinta yadda wasu malaman ke wa'azi tare da yaudarar al'ummar Musulmai a kan basu yadda akwai cutar coronavirus din ba kwata-kwata.
Acewar kungiyar, "ya zama dole a matsayinmu na al'umma da mu kaicewa duk wani Abu da zai maimaita abin da ya faru a Italiya inda cutar tayi kamari. Mutane ne suka bijirewa gargadin masana kiwon lafiya a kan cutar."
DUBA WANNAN: Annobar coronavirus: Gwamnatin tarayya ta shigar da karar wasu manyan shaguna 4 saboda kara farashin kaya
Kungiyar ta kara da nesanta kanta da abinda ta kira da karamin tunanin malamai game da duniya, wanda ta ce rashin fahimtarsa babbar illa ce ga lafiya da zai jefe al'umma cikin hatsari.
Ta kara da cewa, ya kamata a fahimci cewa batun annoba ba sabon abu bane a tarihin duniya. Ta kara da bada misalai da dama na abubuwan da suka faru a tarihi tun zamanin Sahabbai da kuma tabi'a wadanda suka gabace mu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng