Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Hadimansa sun yi bauta ta kafafen zamani

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Hadimansa sun yi bauta ta kafafen zamani

Mun samu labari daga fadar shugaban kasar Najeriya cewa a jiya mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bi hudubar Lahadi ta shafin yanar gizo.

Yemi Osinbajo da Hadimansa sun bi ibadar da aka yi a Ranar Lahadi, 29 ga Watan Maris, 2020, a cocin da ke fadar shugaban kasa ne ba tare da sun halarci cocin ba.

Mai girma mataimakin shugaban kasar da kuma Mukarrabansa wanda ke bin addinin Kirista sun bi matakan da hukumomin lafiya su ka sa na haramta cunkoso.

Idan ba ku manta ba, bayan barkewar cutar Coronavirus a Najeriya, hukumar NCDC ta umarci ‘Yan Najeriya su rika kauracewa shiga cikin dandazo da taron jama’a.

Mai taimakawa mataimakin shugaban kasar wajen harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Laolu Akande, ya bayyanawa ‘Yan jarida wannan a birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: NCDC: Za a fara gwajin COVID-19 a jihohin Kano da Sokoto

Laolu Akande ya ce Mai gidan na sa watau Yemi Osinbajo ya bi ibadar da aka yi ne ta yanar gizo domin bin matakan da hukumar rage yaduwar cuta a Najeriya ta kafa.

Akande ya rubuta: “Yanzu nan mu ka gama ibadar Ranar Lahadi daga cocin Aso Villa ta shafin yanar gizo, inda Mabiya su ka bi sahu daga cikin dakunan gidajensu”

Tun kafin yanzu dai Farfesa Osinbajo ya kebe kansa daga bainar jama’a inda ya cigaba da aiki daga ofishin cikin gidansa, bayan ya yi gwajin kwayar cutar COVID-19.

A karshe Akande ya nuna cewa ya na sa ran za a shawo kan annobar da ta kashe mutum 30, 000 a Duniya. “Muddin Ubangiji na nan, za mu ga karshen COVID-19.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng