An sallami mutane biyar da suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya

An sallami mutane biyar da suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya

A ranar Litin ne gwamnatin jihar Legas ta sallam wasu mutane biyar daga cibiyar killacewa da ke asibitin cututtuka masu yaduwa a unguwar Yaba bayan an tabbatar da cewa yanzu basa dauke da kwayar cutar coronavirus.

Ya zuwa yanzu an sallami jimillar mutane 8 kenan daga cibiyar.

Mutanen da aka sallama suna cikin koshin lafiya, babu alamar gajiya ko damuwa a tare da su, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Duk da mutanen da aka sallama sun zabi a sakaya sunayensu, sun bayyana jin dadi da gamsuwarsu a kan irin kulawar da suka samu a cibiyar.

A yayin da suke mika godiya ga gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, bisa gudunmawa da kokarinsa na ganin an shawo kan annobbar cutar covid-19, mutanen sun nemi hukuma ta kara kyautatawa ma'aikatan cibiyar.

An sallami mutane biyar da suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya

An sallami mutane biyar da suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya
Source: UGC

Da yake magana da manema labarai, daya daga cikin wadanda aka sallama ya ce, "an kawoni wannan cibiya a ranar 15 ga wata bayan sakamakon gwajin da aka yi min ya nuna cewa ina dauke da kwayar cutar.

DUBA WANNAN: Warwas: Man fetur ya yi faduwar da bai taba irinta ba a cikin shekaru 18

"Da farko na fuskanci kalubale amma daga bisani komai ya daidaita. Ma'aikatan cibiyar sun yi matukar kokari wajen bamu kulawa, ni da abokaina shaida ne a kan hakan."

Ya bawa jama'a kwarin gwuiwar cewar kar su wani firgita saboda kwayar cutar coronavirus saboda ana warkewa, alamar da ke nuna cewa za a samu galaba a kan kwayar cutar.

A ranar Lahadi ne hukumar kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa wasu mutane 66 da suka kamu da kwayar cutar coronavirus sun warke.

Sanarwar na kunshe ne a cikin sakon da babbar jaridar kasar Saudiyya da ake wallafa wa cikin harshen turanci; 'Saudi Gazette' ta fitar ranar Lahadi.

Akwai kimanin mutum 96 da aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar coronavirus a kasar Saudiyya tare da asarar rayukan mutane 8.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel