Hukumar NCDC za ta gina dakunan gwajin COVID-19 a Kano da Jihohi 6

Hukumar NCDC za ta gina dakunan gwajin COVID-19 a Kano da Jihohi 6

Mun samu labari cewa hukumar nan ta NCDC mai takaita yaduwar cuta a Najeriya za ta kara yawan dakunan gwajin cutar Coronavirus a fadin kasar nan.

Rahotanni sun zo mana a Ranar Litinin cewa gwamnatin tarayya za ta gina wurare da za a rika gudanar da gwajin kwayar cutar Coronavirus a Jihohi bakwai.

Wadannan Jihohi su ne Ebonyi, Borno, Kano, Sokoto, Ribas, Filato da kuma jihar Kaduna. Hukumar NCDC ta bayyana wannan ne a kan shafinta na Tuwita.

Za a gina wadannan sababbin dakunan gwajin cutar ne a Garuruwan Maiduguri, Fatakwal, Jos da sauran manyan biranen wadannan Jihohin Najeriya da aka ambata.

Kamar yadda mu ka samu labari, NCDC za ta fara ne da ginin dakin gwajin a Garin Ebonyi domin a iya yi wa wadanda ake zargin sun kamu da cutar a Yankin gwaji.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus ta sa Israila ta yi gaba da ‘Yan kasarta daga Najeriya

Hukumar NCDC za ta gina dakunan gwajin COVID-19 a Kano da Jihohi 6
Babu dakunan gwajin kwayar cutar COVID-19 a Arewa
Asali: Facebook

A kaf Yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Arewa ta tsakiya da Kudu maso Gabas, babu inda ake gudanar da wannan gwaji na kwayar cutar COVID-19.

Da wannan shiri da gwamnatin tarayya ta ke yi, dakunan gwajin cutar za su kara yawa daga shida zuwa 13. Wannan zai taimaka wajen yakar wannan annoba.

Ana sa ran cewa za a kammala wannan aiki ne a cikin makonni uku. A halin yanzu dai akwai dakunan gwajin ne a Legas, Ibadan, Osun, Edo da kuma birnin tarayya.

A jihar Legas akwai dakunan gwajin har biyu, don haka yanzu NCDC ta yi azamar kai wannan dakunan gwaji zuwa sauran bangarori musamman Arewacin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng