Warwas: Man fetur ya yi faduwar da bai taba irinta ba a cikin shekaru 18

Warwas: Man fetur ya yi faduwar da bai taba irinta ba a cikin shekaru 18

A ranar Litinin ne farashin gangar danyen man fetur ya fadi warwas zuwa kasa da dalar Amurka 20 sakamakon barazanar da annobar kwayar cutar coronavirus ke cigaba da yi wa tattalin arzikin duniya.

Masana tattalin arziki da mabiya tarihi sun bayyana cewa farashin man fetur bai taba fuskantar irin wannan kaskanci ba a cikin shekaru 18 da suka gabata. Ana ganin cewa farashin zai kara faduwa kasa da haka saboda har yanzu cutar coronavirus na cigaba da mamaya tare da durkusar da tattalin arzikin mutane da kasashe.

"Farashin mai yanzu ya yi matukar wulakantar da yasa babu wata riba da kamfanonin sarrafa man fetur ke samu," a cewar wani kwararren masanin harkokin kasuwancin duniya.

"Bukatar man fetur ta matukar dusashe saboda takaita zirga-zirgar mutane da bukatar su nesanta da juna sakamakon bullowar annobar cutar coronavirus," a cewar Giovanni Staunovo, masanin kasuwancin man fetur.

Warwas: Man fetur ya yi faduwar da bai taba irinta ba a cikin shekaru 18

Man fetur ya yi faduwar da bai taba irinta ba a cikin shekaru 18
Source: Depositphotos

Ana ganin cewa kasashen da ke da arzikin man fetur za su rage yawan adadin danyen man da suke fitar da shi zuwa kasuwar duniya saboda yadda farinjininsa ya sauka da kaso 20% idan aka kwatanta da yadda yake da farinjini a shekarar 2019.

DUBA WANNAN: COVID-19: abinda Dangote ya fada bayan sakamakon gwajinsa ya fito

Karyewar farashin man fetur ne a kasuwar duniya ya sa gwamnatin Najeriya ta rage N25 a farashin litar mai da ake sayarwa a gidajen man da ke fadin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel