Ka bani naira biliyan 1 domin na yaki Coronavirus – Gwamnan Anambra ga Buhari

Ka bani naira biliyan 1 domin na yaki Coronavirus – Gwamnan Anambra ga Buhari

Gwamnan jahar Anambra dake yankin kudu maso gabashin Najeriya, watau yankin Inyamurai, Willie Obiano ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi taimakon naira biliyan 1 don ya yaki annobar Coronavirus a jaharsa.

Jaridar Punch ta ruwaito har yanzu ba’a samu bullar cutar a jahar Anambra, amma tuni gwamnan ya bude wata asusun kudi na musamman a shirinsa na karbar tallafin kudi domin yaki da annobar Coronavirus a jahar.

KU KARANTA: Siyasa ba da gaba ba: Atiku ya jajanta ma El-Rufai bayan kamuwa da Coronavirus

Ka bani naira biliyan 1 domin na yaki Coronavirus – Gwamnan Anambra ga Buhari

Ka bani naira biliyan 1 domin na yaki Coronavirus – Gwamnan Anambra ga Buhari
Source: UGC

Kwamishinan watsa labaru da wayar da kawunan jama’a na jahar, Don Adinuba ne ya bayyana haka, inda yake gwamnan ya dauki wannan mataki ne domin tabbatar da annobar bata shiga jaharsa ba.

Don haka ya roki gwamnatin tarayya ta ba shi tallafin naira biliyan 1 daga cikin kudaden da aka tara don tabbatar da cutar bata shiga jahar ba, saboda a cewarsa jama’an jahar Anambra suna da muhimmanci a Najeriya duba da kwarewarsu wajen kasuwanci.

Sanarwar ta bayyana cewa: “Gwamna Obiano yana ganin dacewar gwamnatin tarayya ta baiwa jahar Anambra naira biliyan 1 sakamakon hadarin da jahar take ciki na samun bullar cutar Coronavirus duba da yawan jama’an dake hada hada a kasuwanninta.

“Muna da akalla kasuwanni 63 a jahar Anambra, daga ciki har da babbar kasuwar Onitsha, wanda ita ce kasuwa mafi girma a yammacin Afirka, a kullum kasuwanninmu na dauke da miliyoyin jama’a daga sassan nahiyar Afirka daban daban, wanda hakan ya sanya jama’anmu cikin hadarin kamuwa da cutar.” Inji shi.

Daga karshe yace gwamnatin jahar ta samar da sabon asusun banki na musamman, kuma gwamnan jahar Willie Obiano ne zai dinga kula da asusun a matsayinsa na shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus a jahar Anambra.

A wani labarin kuma, Gwamnan jahar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ya bayyana cewa ya sadaukar da albashinsa na watanni 10 domin ganin an dakatar da yaduwar annobar Coronavirus a Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel