Coronavirus: Gwamnatin Israila ta dauke Mutanenta da wasu Jakadu a Garin Abuja

Coronavirus: Gwamnatin Israila ta dauke Mutanenta da wasu Jakadu a Garin Abuja

A Ranar Lahadi, 29 ga Watan Maris, 2020, mu ka samu labari cewa gwamnatin kasar Israila ta dauke ‘Yan kasarta fiye da 200 da ke zaune a cikin Najeriya.

Gwamnatin Israila ta dauki wannan mataki ne a sakamakon barkewar annobar Coornavirus. Yanzu haka mutane fiye da 100 su ka kamu da wannan cuta.

A cewar gwamnatin kasar wajen, ta dauki wannan mataki ne domin kare mutanenta daga kamuwa da cutar COVID-19 wanda ta ke hallaka Bayin Allah.

Mista Yotam Kreiman shi ne wanda ya sa-ido wajen dauke Israiliyawan daga kasar. Kreiman shi ne mataimakin shugaban Jakadan kasar Israila a Najeriya.

Yotam Kreiman ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa ya zama dole su dauke mutanensu ganin yadda annobar COVID-19 ta ke cigaba da ratsa kasashe a fadin Duniya.

KU KARANTA: Mutane 111 su ke dauke da kwayar cutar COVID-19 a Najeriya

Channels TV ta ce Jakadan ya shaidawa Manema labarai wannan ne a babban filin sauka da tashin jiragen saman da ke birnin tarayya Abuja a Ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce wani jirgin saman ‘Yan kasuwa da aka yi haya daga Najeriya ne zai dauke mutanen daga babban birnin tarayya Abuja zuwa kasar Israila.

Wannan ne karon farko da jirgi zai tashi daga Najeriya zuwa Israila kai-tsaye. Channels TV ta ce mutanen Israila da aka dauke daga Garin Abuja sun haura 270.

Daga cikin wadanda aka dauka akwai Ma’aikatan Jakadancin Israila, da sauran mutanen kasar da ke aiki a kamfanoni da gudanar kasuwanci a cikin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel