Buhari ya fito da tsare-tsare, ya rufe Jihohi 3, ya yi wa masu biyan bashi lamuni

Buhari ya fito da tsare-tsare, ya rufe Jihohi 3, ya yi wa masu biyan bashi lamuni

A Ranar Lahadi, 29 ga Watan Maris, 2020, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa ‘Yan kasarsa jawabi game da annobar cutar COVID-19 da ta addabi Jama’a.

Jaridar Daily Trust da manyan batutuwan da shugaban kasar ya yi magana a kansu a jawabin na sa. Ga wasu daga cikin kanun jawabin na shugaba Muhammadu Buhari:

1. Gwamnatin Tarayya ta rufe babban birnin tarayya da kuma jihohin Legas da Ogun domin rage yaduwar wannan cuta ta Coronavirus (COVID-19).

2. Shugaba Buhari ya bayyana cewa babbar hanyar kare-kai daga wannan cuta ita ce gujewa cunkuson jama’a da kuma tsabtace jiki daga kwayar cutar.

3. Gwamnatin Najeriya ta kirkiri sababbin dabarun kiwon lafiya, tare da garkame iyakokin kasa. Haka zalika an kawo wasu tsare-tsaren tattalin arziki.

4. Shugaban kasar ya yi kira ga jama’a su dauki shawarar ma’aikatar lafiya da hukumar NCDC domin kare kansu daga kamuwa da cutar COVID-19.

KU KARANTA: Cutar Coronavirus ta kama Abba Kyari, da Gwamnonin Arewa 2

Buhari ya fito da tsare-tsare, ya rufe Jihohi 3, ya yi wa masu biyan bashi lamuni

Buhari ya yi wa 'Yan Najeriya jawabi a kan yaki da COVID-19
Source: Twitter

5. Gwamnatin Buhati ta fitar da Naira biliyan 15 da za ayi amfani da su wajen hana yaduwar wannan cuta. An kuma umarci Jihohin Najeriya su tashi tsaye.

6. Duk da an hana zirga-zirga a wasu bangarori, gwamnati ta ce Malaman kiwon lafiya da Jami’an tsaro da wasu muhimman Ma’aikata za su rika zuwa aiki.

7. Buhari ya ce za a dauke ma’aikatan lafiya da ke aiki a filin sauka da tashin jirgin sama a Abuja da Legas. Kuma Gwamnati ta hana jiragen sama tashi a kasar.

8. Shugaban kasa Buhari ya yi alkawarin kai kayan bada agaji ga Mazauna Yankin Abuja, Legas da Ogun, a sanadiyyar hana jama’an wuraren fita da aka yi.

9. An dakatar da karbar bashin da ke kan wadanda su ke cikin tsarin TraderMoni, MarketMoni da FarmerMoni da sauran tsare-tsaren aron kudin gwamnati.

10. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa kokarin da Malaman kiwon lafiya su ke yi a fadin Najeriya na ganin an kawo karshen annobar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel