Coronavirus: Abba Kyari ya yi magana game da halin da ya ke ciki, ya koma Legas

Coronavirus: Abba Kyari ya yi magana game da halin da ya ke ciki, ya koma Legas

Shugaban ma'aikatatn fadar Shugaba Muhammadu Buhari, Mallam Abba Kyari da ya kamu da kwayar cutar Covid-19 ya isa Legas kamar yadda likitocinsa suka ba shi shawara inda yanzu ya ke samun kulawa.

An tafi da Abba Kyari zuwa Legas ne cikin jirgin sama na daukan marasa lafiya duk da cewa kawo yanzu bai fara nuna alamun kamuwa da kwayar cutar ba kamar yadda This Day Live ta ruwaito.

A daren jiya Lahadi ne Kyari ya fitar da sanarwar cewa likitocinsa sun bayar da shawarar a tafi da shi Legas domin kara yi masa wasu gwaje-gwaje da kuma kulawa da shi.

Kyari ya ce baya jin wasu alamomin cutar a jikinsa kuma ya bin dukkan dokoki da ka'idoji da likitoci suka umurci wadanda suka kamu da cutar su rika bi.

Coronavirus: A karo na farko, Abba Kyari ya yi magana game da halin da ya ke ciki
Coronavirus: A karo na farko, Abba Kyari ya yi magana game da halin da ya ke ciki
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska zuwa gidan yari

Ya bayyana cewa yana yin ayyukansa daga gida kuma ya yi fatar cewa nan da da dadewa ba zai dawo aikinsa.

Ya kuma yaba wa ma'aikatansa na ofishinsa da ya ce suna aiki ba dare ba rana domin yi wa shugaban kasa da kasarsu hidima.

Wani sashi daga cikin sakon da ya wallafa ta ce: "Na rubuta wannan sakon ne domin in sanar da ku cewa likitoci sun bayar da shawarar a tafi da ni Legas domin kara yin wasu gwaje-gawaje da kulawa. Wannan mataki ne kawai na kariya. Lafiya kalau na ke jin jiki na amma a makon da ta gabata sakamakon gwaji ya nuna ina dauke da coronavirus da ke yaduwa a fadin duniya. Na bi dokokin da gwamnati ta bayar na killace kai na.

"Na yi kokarin daukan nauyin kulawa da kai na domin gujewa daura wa bangaren lafiya nauyi duba da cewa a halin yanzu ayyuka sun musu yawa. Kamar sauran mutane da suke dauke da kwayar cutar, bana jin zazabi mai tsanani ko wasu alamomi da ake dangantawa da cutar kuma ina aiki daga gida. Ina fatar zan dawo aiki nan ba da dadewa ba."

Kyari ya mika godiyarsa ga ma'aikatan lafiya da ke kulawa da shi da sauran al'umma da ke masa fatar alheri.

Ya shawarci al'ummar kasa su cigaba da yin takatsantsan tare da bin shawarwarin kwararru da masana a fanin kiwon lafiya su kuma takaita cudanya da juna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164