COVID-19: abinda Dangote ya fada bayan sakamakon gwajinsa ya fito

COVID-19: abinda Dangote ya fada bayan sakamakon gwajinsa ya fito

Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya sanar da cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar COVID-19.

An ji tsoron cewa Dangote zai iya kamuwa da kwayar cutar coronavirus bayan ya yi mu'amala da Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da aka tabbatar da cewa yana dauke da kwayar cutar.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita, Dangote ya bayyana cewa ya yi gwajin ne a matsayinsa na dan kasashe da dama sannan shugaba a kasuwanci.

Ya ce yana jagorantar shugabannin a bangaren kasuwanci domin taimakon gwamnati a kokarinta na dakile yaduwar cutar.

Dangote ya bayyana cewar annobar cutar coronavirus ta taba lafiyar jama'a da sauran harkokinsu.

A ranar Lahadi ne kasar Andolus (Spain) ta sanar da mutuwar mutane 838 sakamakon kamuwa da kwayar cutar coronavirus.

Ya zuwa yanzu, kwayar cutar coronavirus ta kashe mutane fiye da 30,000 a fadin duniya a karshen makon nan. Kwayar cutar ta fi gigita kasar Amurka da yankin nahiyar turai a 'yan kwanakin baya bayan nan.

DUBA WANNAN: Jerin jihohin Najeriya 12 da aka tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus

A wata kididdiga da jami'ar 'Johns Hopkins' ta gudanar, ta bayyana cewa mutane 30,800 ne kwayar cutar COVID-19 ta halllaka a fadin duniya, yayin da take cigaba da mamaya da karya tattalin arzikin mutane da na kasashe.

Mutane fiye da 20,000 ne kwayar cutar ta hallaka a iya yankin nahiyar turai. Kwayar cutar ta kashe mutane fiye da 1400 a rana daya a kasar Spain da Italy.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel