Rade-radi: COVID-19 ta kama Abdullahi Mukhtar, Hadimin Abba Kyari

Rade-radi: COVID-19 ta kama Abdullahi Mukhtar, Hadimin Abba Kyari

Rahotanni daga Jaridar Sahara Reporters sun bayyana cewa Abdullahi Moukhtar, wani Surukin Malam Mamman Daura ya kamu da muguwar cutar nan ta COVID-19.

Jaridar ta bayyana cewa Malam Abdullahi Moukhtar ya na cikin Abokan aikin Abba Kyari da su ka kamu da wannan cuta, amma ake kokarin yi wa lamarin rufa-rufa.

Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya kamu da wannan cuta ta Coronavirus bayan ya ziyarci kasar Jamus da kuma Masar makonnin da su ka wuce.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, wasu Ma’aikatan fadar shugaban kasa da ke aiki a karkashin COS Abba Kyari, sun kamu da wannan cuta ta COVID-19.

Jaridar ta bayyana cewa Moukhtar ya na cikin ma’aikatan fadar shugaban kasa da aka gano sun kamu da wannan cuta. An tabbatar da haka ne bayan an yi masu gwaji.

KU KARANTA: Kyari da sauran Manyan mutanen da COVID-19 ta kama a Najeriya

Rade-radi: COVID-19 ta kama Abdullahi Mukhtar, Hadimin Abba Kyari

Cutar COVID-19 ta kama wasu daga cikin Masu taimakawa Abba Kyari
Source: Facebook

Sahara Reporters ta ce an ki bayyanawa Duniya ainihin abin da ke faruwa ne saboda gudun hankalin na kusa da jami’in fadar shugaban kasar Najeriyar ya tashi.

A cewar Jaridar, Moukhtar ya na rike da mukamin SA a ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar, ma’ana ya na cikin masu taimakawa Malam Kyari.

Rahotannin sun ce mutane uku da ke aiki da Kyari ne su ka kamu da kwayar cutar. Abdullahi Moukhtar wanda ya na cikinsu, Suruki ne a wajen Mamman Daura.

Ana zargin cewa Malam Mamman Daura ya na cikin masu rike da madafan iko a gwamnatin nan ta Buhari. Daura ‘Danuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel