Tashin hankali: Coronavirus ta kashe mutane fiye da 800 a rana daya a kasar Andolus

Tashin hankali: Coronavirus ta kashe mutane fiye da 800 a rana daya a kasar Andolus

A ranar Lahadi ne kasar Andolus (Spain) ta sanar da mutuwar mutane 838 sakamakon kamuwa da kwayar cutar coronavirus. Ya zuw yanzu kawayar cutar coronavirus ta kashe mutane 6,528 a kasar ta Spain.

Yawan adadin mutanen da suka kamu da kwayar cutar coronavirus a kasar Spain ya kai 78,797, lamarin da ke nuna cewa an samu karuwar kaso 9.1 na adadin mutanen da ke kamuwa da kwayar cutar COVID-19 kowacce rana a kasar.

Ya zuwa yanzu, kwayar cutar coronavirus ta kashe mutane fiye da 30,000 a fadin duniya a karshen makon nan. Kwayar cutar ta fi gigita kasar Amurka da yankin nahiyar turai a 'yan kwanakin baya bayan nan.

A wata kididdiga da jami'ar 'Johns Hopkins' ta gudanar, ta bayyana cewa mutane 30,800 ne kwayar cutar COVID-19 ta halllaka a fadin duniya, yayin da take cigaba da mamaya da karya tattalin arzikin mutane da na kasashe.

Mutane fiye da 20,000 ne kwayar cutar ta hallaka a iya yankin nahiyar turai. Kwayar cutar ta kashe mutane fiye da 1400 a rana daya a kasar Spain da Italy.

Tashin hankali: Coronavirus ta kashe mutane fiye da 800 a rana daya a kasar Andolus

Coronavirus ta kashe mutane fiye da 800 a rana daya a kasar Andolus
Source: UGC

Pablo Rodriguez, ma'aikacin lafiya a asibitin birnin Madrid, ya bayyana cewa abin tsoro ne ganin yadda jama'a ke tururuwar asibiti sakamakon kamuwa da kwayar cutar COVID-19.

DUBA WANNAN: Mugun ciwo ne, ina jin jiki; ku tayani da addu'a - Matar da ta kamu da coronavirus

Wasu jami'an lafiya a nahiyar turai sun yi hasashen cewa har yanzu da sauran 'rina a kaba' dangane da barnar da kwayar cutar COVID-19 ke tafkawa.

Tun farkon samun bullar kwayar cutar coronavirus a Najeriya ta hannun wani dan kasar Italiya, an tabbatar da samun kwayar cutar a jihohin Najeriya 12.

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, amma adadin masu dauke da cutar ya kai mutum 96, kamar yadda kididdigar cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta nuna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel