Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar shiga da fice, Babandede, ya kamu da Coronavirus

Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar shiga da fice, Babandede, ya kamu da Coronavirus

Kwantrola Janar na hukumar shiga da ficen Najeriya, Muhammad Babandede, ya kamu da cutar Coronavirus. Jaridar Punch ta ruwaito.

Kwantrolan wanda ya bayyana hakan ta silar sakon Whatsapp da safen nan ya bayyana cewa tuni ya killace kansa tun lokacin da ya dawo daga kasar Birtaniya ranar 22 ga Maris.

Yace, “A yau, an tabbatar na kamu da cutar COVID-19. Tuni na killace kaina tun lokacin da na dawo daga kasar Birtaniya ranar Lahadi 22 na watan nan ta jirgin British Airways a Legas.

“Ina kira ga masoyana, jamian hukumar shiga da fice, da yan Najeriya su taimaka min da wadanda suka kamu da addua.”

Ya kara da cewa “Lokacine mai wuya amma ba zamu iya canza abinda Allah ya kaddara mana ba.”

Babandede ya yi kira da ma’aikatansa su cigaba da bada hadin kai ga mataimakinsa domin ciyar da hukumar gaba.

KU KARANTA Muhammadu Sanusi II da Iyalinsa ba su dauke da COVID – 19 inji ‘Dansa

Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar shiga da fice, Babandede, ya kamu da Coronavirus

Babandede
Source: UGC

A bangare guda, Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane takwas da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Asabar inda tace: “An tabbatar da mutane takwas sun kamu da #COVID19 a Najerya. 2 a Abuja, 4 a Oyo, 1 a Kaduna, 1 a Osun.“

“Misalin karfe 10:40 na ranar 28 ga Maris, an samu mutane 97 da aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami uku, kuma daya ya rigamu gidan gaskiya.“

Ge jerin bullar a jihohi

Lagos- 59

FCT- 16

Ogun- 3

Enugu- 2

Ekiti- 1

Oyo- 7

Edo- 2

Bauchi- 2

Osun-2

Rivers-1

Benue- 1

Kaduna- 1

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel