Wuraren da Gwamna El-Rufai ya sa kafa kafin ya yi gwajin cutar COVID-19
A halin yanzu ta tabbata cewa Mai girma gwamnan jihar Kaduna watau Nasir El-Rufai ya na dauke da cutar COVID-19 bayan fitowar sakamkon gwajin da ya yi a kwanakin baya.
Jaridar Daily Trust ta fitar da wani rahoto inda ta bayyana jerin ayyukan da Malam Nasir El-Rufai ya yi a kafin a gane cewa ya na dauke da kwayar wannan cuta mai hana numfashi.
Mai girma gwamna Nasir El-Rufai ya daurawa mataimakiyarsa Dr. Hadiza Balarabe nauyi a ‘yan kwanakin nan, inda ya nada ta shugabar kwamitin yaki da COVID-19 a Kaduna.
Kafin nan a Ranar 18 ga Watan Maris, gwamnan ya halarci taron gwamnonin Najeriya. Gwamnan Bauchi, Bala A. Mohammed wanda ya ke dauke da cutar, ya halarci wannan taro.
Washegari kuma Nasir El-Rufai ya zauna da mataimakin shugaban kasa da wasu kusoshin gwamnati da jami’an babban bankin Duniya wajen taron majalisar tattalin arziki.
KU KARANTA: COVID-19: Tinubu ya roki Gwamnatin Najeriya ta dakatar da VAT

Asali: Facebook
A Ranar 23 ga Watan Mairs, gwamnan ya yi wani jawabi inda ya dakatar da ma’aikatan gwamnati daga zuwa ofis, ya kuma bukaci jama’a su zauna a gida na tsawon kwanaki 30.
A cikin tsakiyar makon da ya gabata, El-Rufai ya jagoranci wani taro na musamman da aka shirya domin dabbaka matakan da za a bi na rage yaduwar cutar COVID-19 a Kaduna.
Duk a wannan taro da ake yi, a kan samu tazara tsakanin manyan gwamnatin domin hana yaduwar cutar. An kuma ga gwamnan tare da Iyalinsa a gida dauke da tsummar fuska.
Har ila yau a cikin wannan makon da ya wuce, gwamna El-Rufai ya kai ziyara zuwa kasuwar Abubakar Gummi da wasu wurare domin tabbatar da cewa jama’a su na zaune a gidajensu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng