COVID-19: Gwamnatin jihar Kaduna za ta gurfanar da malamai biyu saboda sallar Juma'a

COVID-19: Gwamnatin jihar Kaduna za ta gurfanar da malamai biyu saboda sallar Juma'a

- Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta damko wasu malaman addinin Musulunci biyu kuma za ta gurfanar dasu

- Ana zarginsu da take dokar jihar ne wacce ta haramta jan jama'a jam'in sallah don gujewa yaduwar muguwar cutar Coronavirus

- Kamar yadda gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Twitter, malaman sune Malam Aminu Umar Usman da kuma Malam Umar Shangel

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta gurfanar da wasu malaman addinin Musulunci biyu a jihar bayan sun ja sallar jam'i. Hakan kuwa ya ci karo da dokar ma'aikatar lafiyar jihar na hana yaduwar coronavirus.

Jihar ta hana duk wani taro wanda ya hada da na shagali ko na addini a matsayin hanyar hana yaduwar muguwar cutar.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, a wallafar gwamnatin jihar na ranar Lahadi a shafinta na twitter, ta ce malaman da za ta gurfanar sun hada da Aminu Umar Usman da Umar Shangel.

COVID-19: Gwamnatin jihar Kaduna za ta gurfanar da malamai biyu na addinin Musulunci
COVID-19: Gwamnatin jihar Kaduna za ta gurfanar da malamai biyu na addinin Musulunci
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Ganduje ya fara yi wa lungu da sakunan Kano feshi

"Gwamnatin jihar Kaduna ta kama malaman addinin Musulunci biyu saboda jam'i da suka ja jama'ar jihar duk da hakan ya take dokar ma'aikatar lafiyar jihar," wallafar ta sanar.

Gwamnatin jihar ta bayyana sunayen malaman da Aminu Umar Usman da kuma Malam Umar Shangel.

A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar ta janyr dokar killace kai ta 1926 inda ta bayyana cewa ta saka dokar ta baci a jihar.

Hadiza Balarabe, mataimakiyar gwamnan jihar, ta ce saka dokar ta bacin ta zama dole don kuwa mazauna jihar sun ki bin dokar da aka saka musu don hana yaduwar muguwar cutar.

"Daga tsakiyar daren Alhamis, 26 ga watan Maris, 2020, dole ne dukkan kama'ar jihar Kaduna su zauna a gida. Babu ofisoshi, wuraren kasuwanci kowanne iri da kuma wuraren bauta da aka amince wa su bude," Balarabe tace.

"Ma'aikatan da aka amince wa su fita aiki sune na ma'aikatar lafiya, masu kashe gobara da kuma jami'an tsaro. Masallatai da majami'u duk za a rufe su don babu sallar jami'i."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel