Likitoci 51 sun mutu a kasar Italiya bayan sun kamu da cutar Corona
Kungiyar likitoci ta kasar Italiya sun tabbatar da mutuwar likitoci 51 da suka mutu baki daya bayan sun kamu da cutar Coronavirus
Likitocin sun mutu ne a ranar Juma'a, a rahoton da CNN ta bayar wanda ta samu daga kungiyar likitocin.
Labarin mutuwar sun ta fito ne bayan shugaban kungiyar likitocin Filippo Anelli, yayi kira ga daukacin likitocin kasar da a basu kayan da za su basu kariya a wuraren aikinsu.
"Abu na farko da ya kamata a fara yi shine a kare ma'aikatan lafiya, domin tabbatar da cewa ba sune suke yada cutar ba. Tura su aiki ba tare da kariya ba kamar tura su filin yaki ne ba tare da makamai ba," Anelli ya bayyanawa Financial Times a ranar Alhamis.
A rahoton da hukumar lafiya ta kasar Italiya ta bayar, sama da ma'aikatan lafiya dubu shida ne suka kamu da cutar ta Coronavirus a kasar.
Kasar Italiya dai ita ce kasar da tafi kowacce kasa a duniya yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar Coronavirus, a cikin mutane dubu tamanin da shida (86,000) da suka kamu da cutar a fadin kasar, sama da mutane dubu tara da dari daya ne suka mutu.
Wannan dai na zuwa ne yayin da kasar Amurka ta bayar da sanarwar kwashe mutanenta daga Najeriya sanadiyyar kara samun yaduwar cutar da ake yi a kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng