Ministocin Buhari 43 sun bada gudunmuwan kashi 50% na albashinsu don yakar Coronavirus– Lai Mohammed
Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya alanta cewa shi da takwarorinsa ministoci sun sadaukar da kasha 50 cikin 100 na albashin watan Maris domin taimakawwa gwamnatin tarayya wajen yakar Coronavirus.
A cewarsa, karamar ministar sufuri, Gbemisola Saraki, ke jagorantar kwamitin gudunmuwar.
A jawabin da Lai Mohammed ya saki ranar Asabar. Minista Gbemi Saraki ta ce sun bada gudunmuwar ne domin taimakawa gwamnatin tarayya wajen kawo karshen annobar COVID19 da ta addabi duniya.
Tace: “Wannan annobar da ta addabi duniya na bukatar kasashe, jihohi na nahiyoyi sun hada karfi da karfe wajen tara dukiya domin taimakawa juna. Wannan zai taimaka wajen yakar abin da wuri.”
Ministocin sun jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari kan matakan da yake dauka wajen yakar annobar Coronavirus a Najeriya.

Asali: UGC
KU KARANTA: Jaruman Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 100, sun yi rashin Soji 29
A bangare guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa manyan yan Najeriya da kungiyoyi da suka tashi tsaye wajen yaki da annobar Covid-19 wacce aka fi sani da coronavirus.
Shugaban kasar a wani jawabi daga kakakinsa, Mista Femi Adesina a Abuja a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris, ya jinjinawa wa mambobin hukumomi masu zaman kansu a Najeriya kan hada kai da suka yi wajen yakar cutar ta Covid-19.
Ya yaba ma mutane kamar haka, Dangote, Abdulsamad Rabiu na gidauniyar BUA, Femi Otedola, Tony Elumelu, Herbert Wigwe, Segun Agbaje da Jim Ovia na UBA, bankunan Access, GTB, Zenith kan gudunmawar naira biliyan daddaya da kowannensu ya bayar.
Ga adadin kudin da suka bada gudunmuwa:
Tony Elumelu UBA - Biliyan 5
Abdulsamad Rabiu BUA - N1bn da kayan asibiti
Femi Otedola - N1bn
Aliko Dangote - N200m
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng