Obasanjo ya bayar da gidanshi na Hilltop kyauta domin a mayar da shi cibiyar duba masu Coronavirus

Obasanjo ya bayar da gidanshi na Hilltop kyauta domin a mayar da shi cibiyar duba masu Coronavirus

- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayar da gidansa dake jihar Ogun domin kula da masu cutar Corona

- Tsohon shugaban kasar ya bayar da gidan ne ga gwamnatin jihar Ogun

- Gidan wanda yake dauke da dakuna 32 da janareto wanda yake aiki babu dare babu rana zai zama cibiyar duba masu cutar

Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayar da gidanshi dake Presidential Hilltop, Abeokuta, cikin jihar Ogun domin a mayar da shi cibiyar lura da masu cutar Coronavirus da ta addabi duniya.

Mai taimakawa Obasanjo a fannin sadarwa, Kehinde Akinyemi, shine ya tabbatar da haka, inda ya ce gidan tsohon shugaban kasar mai dauke da dakuna 32 dake Presidential Boulevard a Oke Sari, dake garin Abeokuta babban birnin jihar Ogun, ya dankashi ga gwamnatin jihar domin a kula da masu cutar. Haka kuma gidan yana dauke da injin janareto da yake aiki babu dare ba rana.

Akinyemi ya kara da cewa:

"Ina ganin duk wanda yake da damar taimakawa a wannan lokaci ta kowacce hanya ya taimaka yayi."

KU KARANTA: Sama da mutane 300 sun mutu yayin da 1000 suke kwance rai a hannun Allah, bayan sun sha wani magani da suke tunanin zai kawar musu da cutar Corona

Wannan dai na zuwa ne yayin da mutane da yawa na Najeriyan da suka hada da 'yan siyasa da hamshakan masu kudi suke bayar da taimakon su domin tallafawa wajen yaki da yaduwar cutar.

Haka a yau mun samu labarin cewa ministocin Najeriya sun bayar da rabin albashinsu na watan Maris dinnan domin a cigaba da yaki da yaduwar cutar a fadin Najeriya.

A Najeriya dai ana cigaba da kara samun yaduwar cutar musamman a jihar Legas wacce take da mafi yawan mutanen da suke dauke da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel