COVID-19: Ganduje ya fara yi wa lungu da sakunan Kano feshi

COVID-19: Ganduje ya fara yi wa lungu da sakunan Kano feshi

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da aikin feshi na musamman a cikin hanyoyin kariyar shigar COVID-19 jihar Kano.

A takardar da sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar, ya ce an kaddamar da feshin ne a ranar Asabar wanda ya zo dai-dai da ranar tsaftace jihar. An fara ne ta kofar gidan gwamnatin jihar.

A takardar, gwamnan ya bayyana cewa shirin feshin ana yinsa ne da hadin guiwa da tallafin Kamfanonin kungiyar Lee a matsayin gudumawarta a jihar.

Gwamnan yayi kira ga sauran 'yan kasuwa masu zaman kansu da su hada kai tare da tallafowa jihar wajen daukar mataki.

COVID-19: Gwamna Ganduje ya fara yi wa lungu da sakon Kano feshi

COVID-19: Gwamna Ganduje ya fara yi wa lungu da sakon Kano feshi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Sabbin mutum 11 sun kamu a Najeriya, jimilla 81

Ya ce: "Wannan na bayyana fara tsaftace jihar ne. Muna yakar annobar ne ta kowanne lungu. Don haka ne muka fara yakarta a muhallinmu. Saboda haka ne ma'aikatar Muhalli ta mayar da hankali."

Ganduje ya bayyana cewa garkame iyakokin jiharsa da yayi ba zai shafi abubuwan da ake bukata na yau da kullum ba kamar kayan abinci, kayan hadin abincin da sauransu, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

"Amma kuma bamu son gurgunta tattalin arzikin jihar na, shiyasa bamu hada da abubuwan da jama'a za su bukata ba. A yayin da muke cikin wannan matsanancin halin, zamu tabbatar da cewa mun rage wahalar da jama'a ke fuskanta," ya bayyana.

Takardar ta bayyana cewa an fara feshin a gidan gwamnatin jihar inda za a gangara asibitin kwararru na Muhammadu Abdullahi Wase da ke GRA Nasarawa.

Wadanda suka kaddamar da feshin sun hada da Kwamishinan muhalli, Dr Kabiru Ibrahim Getso da Muhammad Garba, babban manajan hukumar tsaftace muhalli da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel