Tashin hankali yayin da rundunar Yansanda ta umarci jami’anta su tashi daga bariki

Tashin hankali yayin da rundunar Yansanda ta umarci jami’anta su tashi daga bariki

Jami’an Yansandan Najeriya dake zama a barikin Yansanda na horas da jami’I masu kula da zirga zirgan ababen hawa a kan titi, Ikeja Legas sun shiga halin fargaba bayan wani umarni daga hukumar Yansanda da ta umarci su tattara inasu inasu su tashi daga barikin.

Punch ta ruwaito wannan umarni na kunshe ne a cikin wata takarda dake dauke da sa hannun mataimakin kwamshina Ajewole Adebayo da kwanan watan 24 ga watan Feburairu, inda ya nemi su tashi zuwa ranar Talata, 31 ga watan Maris, ko kuma a fitar dasu da karfi da yaji.

KU KARANTA: Gwamnan Nasarawa, mataimakinsa da Sarkin Lafiya sun tsira daga Coronavirus

Takardar ta ce: “Da wannan wasikar ake umartarku ku tashi daga rukunin gidajen ma’aikata da dakunan dake kwalejin horas da jami’an kula da zirga zirgan ababen hawa dake Ikeja zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2020.

“Ku sani zamanku a harabar kwalejin ya haramta, don haka idan baku tashi zuwa wannan rana ba, za’a fitar daku da karfin tuwo, kuma zaku fuskanci hukunci.”

Sai dai Yansanda da dama sun bayyana rashin adalcin dake tattare da wannan umarni, inda suka ce sai dai suka bi duk hanyoyin da ake bi wajen neman gidajen, da kuma cika dukkanin sharuddan da ake cikawa don samu, amma kwatsam dare daya za’a rabasu da muhallansu.

Guda daga cikin su, wanda ke da yara hudu ya nuna takardar da kwamandan kwalejin horas da Yansanda ya bashi na izinin zama a gidan, don haka yace sun yi mamakin tashinsu da aka yi ba tare da wata kwakkwaran dalili ba.

Bugu da kari yace an fada musu wai babban sufetan Yansanda ne ya bada umarnin tashinsu, amma sun tambayi wasu na kusa da sufetan, sun tabbatar musu da cewa sufetan ba shi da masaniya game da umarnin.

Koda majiyar Legit.ng ta tuntubi shugaban kwalejin, Adebayo a kan batun, sai ya turasu wajen mai magana da yawun Yansandan Najeriya, Frank Mba, shi kuma bai dauki kiraye kirayen da aka yi masa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel