Sama da mutane 300 sun mutu yayin da 1000 suke kwance rai a hannun Allah, bayan sun sha wani magani da suke tunanin zai kawar musu da cutar Corona

Sama da mutane 300 sun mutu yayin da 1000 suke kwance rai a hannun Allah, bayan sun sha wani magani da suke tunanin zai kawar musu da cutar Corona

Sama da mutane 300 ne suka mutu a kasar Iran yayin da sama da mutane 1000 ke kwance rai a hannun Allah bayan sun sha wani magani da a tunaninsu zai kare su daga kamuwa da cutar Coronavirus

Bayan rahoton ruwan sinadari na wanke hannu da yake kare mutane daga kamuwa daga cutar, kafafen sadarwa a kasar Iran sun dinga wallafa wani rahoto cewa wata barasa da aka hada da wani kalar sinadari tana magani kuma tana kare mutane daga kamuwa da cutar Coronavirus.

Sama da mutane 300 sun mutu yayin da 1000 suke kwance rai a hannun Allah, bayan sun sha wani magani da suke tunanin zai kawar musu da cutar Corona

Sama da mutane 300 sun mutu yayin da 1000 suke kwance rai a hannun Allah, bayan sun sha wani magani da suke tunanin zai kawar musu da cutar Corona
Source: Facebook

A yadda fox news ta ruwaito, bayan wani rahoto na kafar sadarwa da ke nuni da cewa wani malamin makaranta a kasar Birtaniya da wasu mutane sun warke daga cutar ta Corona bayan sun hada zuma da giya, sai wani kamfani ya fara kaiwa 'yan kasar Iran din giya, inda ake sanar da su cewa tana maganin Coronavirus, hakan ya zo ne kuma duk da cewa a Musulunce an haramta shan giya.

KU KARANTA: IG na 'yan sanda ya bada umarnin hukunta jami'an 'yan sanda da bidiyonsu ke yawo suna yiwa mutane barna a shaguna

"Sauran kasashe suna da matsala daya suma, wacce take annobar Coronavirus," cewar Dr Hossein Hassanian, mai bawa ministan lafiya na kasar Iran shawara.

"Yanzu dole sai mun nemawa mutane lafiya daga matsalar giya mai guba da suka sha, sannan kuma mu nema musu maganin Coronavirus," cewar Hassanian.

"Cikin rashin sa'a a wasu jihohin mutanen da suka mutu sanadiyyar shan wannan giya mai guba ya dara yawan mutanen da cutar ta Coronavirus ta kashe," Hassanian ya kara da cewa.

A yanzu haka dai kasar Iran tana da yawan mutane 29,000 da suke dauke da cutar yayin da sama da mutane 2,200 suka rasa rayukansu, sai dai hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa akwai yiwuwar kasar Iran ba ta bayar da rahoto na gaskiya akan lamarin dake faruwa a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel