COVID-19: Sakamakon gwajin majinyata 6 ya nuna sun warke - Sanwo-Olu

COVID-19: Sakamakon gwajin majinyata 6 ya nuna sun warke - Sanwo-Olu

- Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce sakamakon gwajin masu cutar coronavirus shida a jihar a yanzu yana nuna basu dauke da ita

- Sanwo-Olu ya sanar da hakan ne yayin da yake bada bayani a kan ci gaban da ake samu game da masu cutar a jihar

- Ya kara da cewa za a sallame su ne kadai idan gwaji na biyu ya bayyana basu dauke da cutar

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce sakamakon gwajin masu cutar coronavirus shida a jihar a yanzu yana nuna basu dauke da ita.

Sanwo-Olu ya sanar da hakan ne yayin da yake bada bayani a kan ci gaban da ake samu game da masu cutar a jihar.

Mataimakinsa na musamman a bangaren kiwon lafiya, Tunde Ajayi ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis. Ya bayyana cewa majiyata shida ne da ke fama da cutar za a sallama daga asibiti.

Sanwo-Olu bai tabbatar da cewa su din bane, ko ba su ba.

COVID-19: Sakamakon gwajin majinyata 6 ya nuna sun warke - Sanwo-Olu

COVID-19: Sakamakon gwajin majinyata 6 ya nuna sun warke - Sanwo-Olu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Ba abinda ya shafi jama'a bane - FG ta yi martani a kan lafiyar Abba Kyari

Ya kara da cewa za a sallamesu ne kadai idan gwaji na biyu ya bayyana basu dauke da cutar.

Ya ce: "A yayin da nake wannan jawabin, muna kokarin tabbatar da cewa wasu mutane biyar ko shida basu dauke da cutar. Za mu tabbatar da hakan ne idan gwaji kashi na biyu ya bayyana basu dauke da cutar. Za a tabbatar da hakan ne a daren yau ko gobe."

Idan zamu tuna, a jiya ne The Cable ta ruwaito cewa majinyata shida da ke fama da cutar coronavirus a jihar Legas ne suka warke. Za a sallame su daga cibiyar killace majinyatan cutuka masu yaduwa da ke Yaba a jihar.

Tunde Ajayi, mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar Legas, ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a ranar Alhamis.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, ya rubuta: "Shida daga cikin majinyatan cutar COVID-19 ne suka warke kuma za a sallamesu nan ba da dadewa ba. Abinda jihar Legas ke yi a yanzu ya sha banban. Mu ne a gaba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel