IG na 'yan sanda ya bada umarnin hukunta jami'an 'yan sanda da bidiyonsu ke yawo suna yiwa mutane barna a shaguna

IG na 'yan sanda ya bada umarnin hukunta jami'an 'yan sanda da bidiyonsu ke yawo suna yiwa mutane barna a shaguna

- Za a hukunta wasu 'yan sanda da bidiyon su yake ta faman yawo a shafukan sadarwa suna yiwa mutane barna a shago

- Shugaban hukumar 'yan sanda na Najeriya, Adamu Mohammed shine ya bukaci rundunar 'yan sandan jihar Legas ta hukunta jami'an da aka kama da hannu a wannan lamari

Shugaban hukumar 'yan sanda na kasa, Adamu Mohammed, ya bayar da umarnin a hukunta jami'an 'yan sandan da aka kama a kyamara suna yiwa mutane barna a shaguna a jihar Legas.

Idan ba a manta ba gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu, ya bayar da umarnin a rufe duk wasu shaguna dake fadin jihar domin kokarin rage yaduwar cutar Corona.

Jami'an 'yan sandan da aka bawa umarnin su fita su duba ko mutane suna bin wannan doka da gwamnan jihar ya bayar, mutane da yawa sun bi wannan umarni, inda wasu kuma suka bijire suka fito harkar kasuwancin su, hakan ya sanya 'yan sandan suke ganin ya kamata su dauki mataki akan wadannan masu shaguna.

Da yake magana game da bidiyon 'yan sandan da yake ta yawo a shafukan sadarwa, shugaban hukumar 'yan sandan ya umarci kwamishinan 'yan sandan jihar Hakeem Odumosu, da yayi gaggawar gabatar da bincike akan wannan lamari sannan kuma ya gaggauta hukunta jami'an da aka kama da hannu a wannan aika-aika.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel