Covid-19: Akwai yiwuwar mutum 39,000 su kamu da cutar a Legas - Kwamishinan Lafiya

Covid-19: Akwai yiwuwar mutum 39,000 su kamu da cutar a Legas - Kwamishinan Lafiya

- A yau Juma'a ne gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa tana tsammanin a kalla mutane 39,000 a jihar za su kamu da cutar COVID-19

- Kwamishinan lafiyar jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana hakan ga manema labarai a ma'aikatar lafiyar jihar da ke Alausa

- Ya kara da bayyana cewa, idan kowa ya dinga nisantar shiga jama'a, akwai yiwuwar ya ragu ya kai 13,000

A yau Juma'a 27 ga watan Maris ne gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa tana hasashen a kalla mutane 39,000 a jihar za su kamu da kwayar cutar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus.

Kwamishinan lafiyar jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana hakan ga manema labarai a ma'aikatar lafiyar jihar da ke Alausa.

Abayomi ya ce, "A hasashen mu muna zaton karshen mummunan lamarin da zamu samu shine mutane 39,000 na jihar Legas su bayyana dauke da cutar."

Ya kara da bayyana cewa, idan kowa ya dinga nisantar shiga jama'a, akwai yuwuwar ya ragu ya kai 13,000.

"Idan muka hada da nisantar juna tare da zakulo wadanda suka yi mu'amala da masu cutar, zamu iya takaita yawan jama'ar da za su samu cutar," in ji shi.

Covid-19: Akwai yiwuwar mutum 39,000 sun kamu da cutar a Legas - Kwamishinan Lafiya

Covid-19: Akwai yiwuwar mutum 39,000 sun kamu da cutar a Legas - Kwamishinan Lafiya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Mu sadaukar da albashinmu na watan Maris - Dan majalisar wakilai

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, Abayomi ya ce wannan yawan jama'ar da ya bayyana kadan ne idan aka dangantata da yawan yadda cutar ke barkewa a duniya.

"Wannan yawan jama'ar da muka sanar zai iya saka tsoro a zukatan jama'a, amma muna sanarwa ne don jama'ar jihar Legas su bi umarni ta yadda zamu gujewa taruka da kuma sauran hanyoyin hana yaduwar cutar," a cewarsa.

"Ku duba lokacin da aka samu mutum daya dauke da cutar, ba zamu gwada yadda masu cutar ke karuwa ba da kasar Spain, Italiya da kuma Iran ba. A lokacin da muka samu mutum daya dauke da cutar, mun dau makonni a kalla hudu kafin mu samu mutane 37 masu cutar," ya kara da cewa

"Amma kuma idan muka duba kasashen Spain, Italiya da Iran, a lokacin da suka kai makonni hudu da bullar cutar, sun samu masu cutar har 20,000. Hakan ke nuna mana cewa muna yin abinda ya dace a jihar nan," Abayomi ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel