Nayi imani da Allah cewa a yanzu aka hadani da mai cutar Coronavirus zai warke - Matashin mai magani dan Kano

Nayi imani da Allah cewa a yanzu aka hadani da mai cutar Coronavirus zai warke - Matashin mai magani dan Kano

A yayin da duniya baki daya ta rude, masana kimiyya suka bazama neman maganin wannan cuta ta kafewar numfashi, an sami wani matashin mai magani a Kano mai suna Malami Jan Wuya, da ya bugi kirji yace shi yana da maganin wannan cuta

Koda yake wasu mutanen na gani cewa zancen nasa yafi kama da shiririta, amma wasu daidaikun mutane na ganin cewa zai fi kyau a bashi dama ya gwada baiwar da Allah yayi masa.

Da aka tambayeshi shin ko ya taba ganin mai cutar a zahiri, sai ya ce: "Nan fa daya, bai taba gani ba," amma ya hakikance da gwamnati za ta kira shi zai nuna irin tashi basirar da Allah yayi masa.

Nayi imani da Allah cewa a yanzu aka hadani da mai cutar Coronavirus zai warke - Matashin mai magani dan Kano
Nayi imani da Allah cewa a yanzu aka hadani da mai cutar Coronavirus zai warke - Matashin mai magani dan Kano
Source: Facebook

KU KARANTA: An yankewa wasu masu Coronavirus hukuncin kisa saboda sunki bin umarnin gwamnati na killace kansu a gida

Ga dai abinda ya ce: "Assalamu Alaikum, yana da kyau dukkanin Musulmai su sani cewar kowacce irin cuta da take a duniya, ba ta sauko ba sai da aka fara saukar da maganinta.

"Saboda haka dan mutum ya fito ya ce yana da maganin wannan cuta ta Coronavirus ba sabon abu bane ba kuma abin mamaki bane.

"Allah ne ya huwace mini, nayi imani da ikon Allah a yanzu aka hadani da mai Coronavirus zai warke.

"Ban taba gwada maganin a jikin kowa ba, hasalima ban taba ganin mai cutar ba, amma na tabbata yanzu aka hadani da mai cutar zan warkar dashi.

"Saboda haka nake kira ga gwamnatin Najeriya dama sauran kasashen duniya baki daya da su kirani su bani dama na gwada bajintar da Allah yayi mini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel