Bayan amshe naira miliyan 7, yan bindiga sun cigaba da rike kansilolin Zamfara

Bayan amshe naira miliyan 7, yan bindiga sun cigaba da rike kansilolin Zamfara

Miyagun yan bindiga da suka yi garkuwa da kansilolin jahar Zamfara guda biyu daga karamar hukumar Gummi sun cigaba da rike kansilolin bayan sun amshe naira miliyan bakwai da aka biya a matsayin kudin fansa.

Jaridar Punch ta ruwaito a watan da ta gabata ne yan bindigan suka yi garkuwa da kansilolin biyu da suka hada da kansilar mazabar Ubandawaki, Lawal Gummi da Sahabi Abubakar kansilar Birin Tudu, sai kuma Murtala Arzika, kansilan mazabar Gayari wanda daga bisani ya tsere.

KU KARANTA: Annobar Corona: Ba zamu dage zaben kananan hukumomi ba – ODIEC

Yan bindigan sun sace kansilolin ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Gusau, kuma tun wannan lokaci suka tubure ba zasu sake su ba har sai an biyasu kudin fansa naira miliyan 40.

Wani dan uwan kansila Sahabi ya bayyana cewa sun hada ma yan bindigan naira miliyan 7, amma bayan sun amshi kudin da alkawarin za su saki kansilolin, sai kawai suka direbansu kadai. “Sa’annan suka nemi mu kawo musu cikon naira miliyan 33.” Inji shi.

Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, SP Mohammed Shehu ya bayyana cewa rundunarsu na iya kokarinta na ganin ta ceto kansilolin, inda yace tun bayan dauke kansilolin, rundunarsu ta ceto akalla mutane 13 daga hannun yan bindiga daga ciki har da dakacin Wuya, Alhji Umaru Usman da dansa.

A wani labarin kuma, shelkwatar tsaro ta kasa ta sanar da wata gagarumar nasara da dakarun Sojin Operation Lafiya Dole suka samu a wani samame da suka kai a wani sansanin samar da horo da na Boko Haram da mayakan ISWAP.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito daraktan watsa labaru na shelkwatar, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.

A cewar Onyeuko, hadakan dakarun rundunar sojan kasa da na rundunar Sojan sama ne suka kai farmakin a ranar Laraba 25 ga watan Maris bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da tattaruwar yan ta’adda a sansanin dake kauyen Matuku a Arewacin Borno.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel